Mutumin Da Yafi Kowa Tsawo a Duniya Ya Nufi Kasar Rasha Don Biɗar Matar Aure

Mutumin Da Yafi Kowa Tsawo a Duniya Ya Nufi Kasar Rasha Don Biɗar Matar Aure

  • Mutumin da yafi kowa tsawo a duniya, Sultan Kosen ya nufi kasar Rasha don neman matar da zai aura kuma ta haifa masa yara
  • A cewarsa ya tafi kasar ne don ya ji labarin yadda matan kasar Rasha suke da matukar kyau da kwarewa a soyayya a ganinsa zai fi dace a can
  • Dama ya taba auren wata mata ‘yar kasar Siriya a shekarar 2013, amma ba su daidaita ba saboda Larabci kadai ta iya shi kuma yaren Turkiyya ya iya

Kasar Rasha - Mutum mafi tsawo a tarihin duniya, Sultan Kosen ya nufi kasar Rasha don nemo matar aure wacce za ta haifa masa yara, The Guardian ta ruwaito.

A farkon watan Disamba Kosen ya tafi Moscow don neman matar aure. A cewarsa ya je Rasha ne saboda yadda ya ji labarin matan kasar su na da kyau da iya soyayya.

Kara karanta wannan

Buba Galadima: Dalilan da suka sa ake ta kame-kame, aka ki amincewa a gyara dokar zabe

Mutumin Da Yafi Kowa Tsawo a Duniya Ya Nufi Kasar Rasha Don Biɗar Matar Aure
Mutumin Da Yafi Kowa Tsawo a Duniya Ya Garzaya Rasha Don Neman Matar Aure. Hoto: Guardian NG
Asali: Facebook

Hakan ya sa ya yanke shawarar amaryarsa ta kasance ‘yar kasar Rasha inda yake so ta haifa masa da namiji da diya mace, rahoon The Guardian.

Ya ce kudi ba matsalarsa bane

Yayin tattaunawa da shirin gidan talabijin na Let Them Speak a ranar Litinin, 20 ga watan Disamba, Kosen ya kada baki ya ce:

“Abu ne mai sauki. Ina da hali don haka kudi ba matsalarmu bane.
“Zan so wucewa da matata kasar Turkiyya. Ina zama ne a wuri mai dumbin tarihi a kudu maso gabas amma kuma ya na da nesa da teku. Na ji matan kasar Rasha su na son hadaddun maza masu da’a. Don haka abu mai sauki ne!”

Ya kara da cewa:

“Macen kasar Rasha tana nuna wa mijinta kauna mai dorewa.”

Kara karanta wannan

A raba mu, duka take lakaɗa min har da damƙar mazakuta na, Magidanci ya yi ƙarar matarsa Fatima

Wata cuta ce yake fama da ita wacce ta janyo masa tsawon

Manomin kasar Turkiyyan mai shekaru 39 ya na fama da wata cuta ne wacce ta ke janyo yana tsawo sosai saboda wasu sinadarai da jikinsa ya ke fitarwa.

Sultan Kosen ya shiga cikin littafin tarihin duniya (Guinness World Record) saboda kasancewarsa mutum mai rai da ya fi kowa tsawo na 8ft 3ins (2.51metres).

Ya ce ya saba da tsawon shi duk da dai yana shan wahalar yin wasu abubuwan.

Ya taba aure dama

Dama Kosen ya taba auren wata ‘yar kasar Siriya, Merve Dibo a shekarar 2013 mai tsawo 5’9; sai dai sun kasa daidaitawa saboda Larabci ta iya yayin da shi kuma yaren ‘yan Turkiyya ya iya.

Ba su dade da rabuwa da Kosen ba, shi yasa yanzu ya koma kasuwa. Bai bayyana kwanakin da zai yi wurin neman mata a kasar Rasha ba.

Matar da ta fi kowa 'tsufa' a duniya ta mutu, tun ƙarni na 19 ta ke raye

Kara karanta wannan

Waiwaye a 2021: Haziƙan Ɗaliban Najeriya 4 Da Suka Karya Tarihin Da Ba a Taɓa Zaton Wani Zai Iya Ba

A wani labarin, kun ji cewa mutanen Philippines sun shiga damuwa bayan mutuwar wata mata, Francisca Susano, wacce ake kyautata zaton ita ce wacce ta fi kowa tsufa a kasar kuma ta kafa tarihi ta zama mafi tsufa a duniya.

Francisca, kamar yadda Daily Star ta ruwaito, ta mutu ne a ranar Litinin, 22 ga watan Nuwamba da misalin 6:45pm tana da shekaru 124 a gidanta da ke Kabankalan a wuraren Negros Occidental, Philippines.

Kafin mutuwarta, Guinness World Records su na shirin gabatar da ita a watan Satumba a matsayin mutum ma fi tsufa a duniya, Daily Mail ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel