Matar da ta fi kowa 'tsufa' a duniya ta mutu, tun ƙarni na 19 ta ke raye

Matar da ta fi kowa 'tsufa' a duniya ta mutu, tun ƙarni na 19 ta ke raye

  • An samu rahotanni akan yadda Farancisca Susano, ta zama matar da ta fi kowa tsufa a duniya inda ta rasu tana da shekaru 124
  • An haifi matar ‘yar Philippines a ranar 11 ga watan Satumban 1897 kuma ta mutu ne da misalin karfe 6:45pm a ranar Litinin, 22 ga watan Nuwamba
  • Duk da dai har yanzu ba a gano abinda ya halaka tsohuwar ba, amma an samu rahotanni wadanda suke nuna alamomin cutar COVID-19

Philippines - Mutanen Philippines sun shiga damuwa bayan mutuwar wata mata, Francisca Susano, wacce ake kyautata zaton ita ce wacce ta fi kowa tsufa a kasar kuma ta kafa tarihi ta zama mafi tsufa a duniya.

Francisca, kamar yadda Daily Star ta ruwaito, ta mutu ne a ranar Litinin, 22 ga watan Nuwamba da misalin 6:45pm tana da shekaru 124 a gidanta da ke Kabankalan a wuraren Negros Occidental, Philippines.

Kara karanta wannan

Shi kaɗai ya san inda na ke ajiye asusun: Budurwa ta faɗa wa kotu saurayin ta ne ya sace mata kuɗi

Matar da ta fi kowa 'tsufa' a duniya ta mutu tana da shekaru 124, tun ƙarni na 19 ta ke raye
Matar da ta fi kowa 'tsufa' a duniya ta riga mu gidan gaskiya. Hoto: Daily Mail
Asali: UGC

Kafin mutuwarta, Guinness World Records su na shirin gabatar da ita a watan Satumba a matsayin mutum ma fi tsufa a duniya, Daily Mail ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro bayanai akan cewa babu wani bayani dangane da silar mutuwarta sai dai an ruwaito yadda aka ga alamun COVID-19 tattare da ita.

Ita ce matar karni na 19 da ta rage a duniya a raye

Ita ce mutum ta karshe daga karni na 19 da ta rayu har ta kai ranar Litinin, dama an haifi Francisca ne a ranar 11 ga watan Satumban 1897.

A kan kira tsohuwar da Lola saboda an haifeta lokacin da Spain tana mulkin mallaka lokacin Sarauniya Victoria na kan karagar mulkin Great Britain.

‘Yan garinsu Francisca sun nuna alhininsu

Kara karanta wannan

Mutane sun tarawa mutumin da ya kwashe shekaru 43 cikin kurkuku kudi, N95m, bayan an gano sharri akayi masa

‘Yan garinsu Francisca sun nuna alhininsu akan mutuwar tsohuwar ta wata takarda da suka saki a ranar Talata, 23 ga watan Nuwamba, garin Kabankalan sun bayyana mutuwar a matsayin labari mara dadi amma su na alfahari da ita.

Wani bangaren takardar ya zo kamar haka:

“Muna bakin cikin samun labarin mutuwar Lola Francisca Susano abar kaunarmu, wacce ta rasu da safiyar Litinin 22 ga watan Nuwamba.
“Mayor Pedro Zayco, Jr., Vice Mayor Raul Rivera da duk wasu masu matsayi a garin Kabankalan su na mika ta’aziyya ga ‘yan uwan Lola a wannan lokacin da suke makokin rashinta.
“Lola Iska za ta ci gaba da zama abar alfaharinmu.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel