Waiwaye a 2021: Haziƙan Ɗaliban Najeriya 4 Da Suka Karya Tarihin Da Ba a Taɓa Zaton Wani Zai Iya Ba

Waiwaye a 2021: Haziƙan Ɗaliban Najeriya 4 Da Suka Karya Tarihin Da Ba a Taɓa Zaton Wani Zai Iya Ba

Ilimi dai kogi ne kamar yadda masu iya magana kan ce kuma kowa akwai iya basira da hazaka da Allah ya bashi a bangarori na rayuwa daban-daban har ma da harkar karatu.

Wadannan daliban sun shiga jami'a ne ba tare da sakamako na a zo a gani ba amma daga bisani suka fita da sakamakon da ya zama abin yabo.

Waiwaye a 2021: Haziƙan Ɗaliban Najeriya 4 Da Suka Kafa Tarihin Da Ba a Taɓa Zaton Wani Zai Iya Ba
Wasu hazikan daliban Najeriya 4 da suka kafa tarihi da ba a taba tsammani ba. Hoto: Chris Kehinde Nwandu, LinkedIn/Ruqayyah Adelakin
Asali: Facebook

A wannan rahoton, Legit.ng ta haskaka tauraronta kan wasu daliban Najeriya 4 da suka yi bajinta a makarantunsu ta hanyar karyaa tarihin da ake ganin ba masu yiwuwa bane.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

1. Fetimi Balogun Bebetebe

Fetimi Balogun Bebetebe ya karya wani tarihi na tsawon shekara 55 da Jami'ar Cebu da ke kasar Philippines.

Kara karanta wannan

Ziyarar Maiduguri: Abubuwa 3 da na ke so magajina ya yi idan ya karbi mulki - Buhari

Waiwaye a 2021: Haziƙan Ɗaliban Najeriya 4 Da Suka Kafa Tarihin Da Ba a Taɓa Zaton Wani Zai Iya Ba
Ya karya tarihin da aka kafa shekara 55 da suka gabata. Photo Credit: Chris Kehinde Nwandu
Asali: Facebook

Matashin wanda gwamnatin tarayyar Najariya ta dauki nauyin karatunsa na digiri a bangaren injiya na jiragen ruwa a karkashin hukumar kula da sifirin jiragen ruwan Najeriya, NIMASA, ya samu sakamako mafi daraja a jami'ar ta kasar waje.

2. Otoko Steven Edwards

Otoko Steven Edwards ya fara nuna bajintarsa ne a Jami'ar Jihar Rivers inda ya kammala digirinsa da makin CGPA 5.0.

Matashin ya yi digirinsa na farko ne a tsangayar koyar da lissafi, inda ya karya tarihin da aka kafa tsawon shekaru 41 a tarihin Jami'ar.

Waiwaye a 2021: Haziƙan Ɗaliban Najeriya 4 Da Suka Kafa Tarihin Da Ba a Taɓa Zaton Wani Zai Iya Ba
Ya karya tarihin da aka kafa shekaru 41 da suka shude.
Asali: Original

Ya sauya ne daga tsangayar karatun injiniya zuwa lissafi bayan ya gano ya fi kaunar lambobi a kan injina.

3. Mbagwu Johnpaul Chiagoziem

A Jami'ar Jihar Imo, Owerri, matashi Mbagwu Johnpaul Chiagoziem ya kafa tarihi bayan ya kammala digiri sa sakamako mafi daraja na 1st Class a 'Industrial Physics' a karon farko bayan shekaru 39.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari za ta ba kamfanin Dangote, BUA da wasu tallafin kudi N30bn

Waiwaye a 2021: Haziƙan Ɗaliban Najeriya 4 Da Suka Kafa Tarihin Da Ba a Taɓa Zaton Wani Zai Iya Ba
Ya karya tarihin da aka kafa shekaru 39 da suka gabata.
Asali: Original

Bajintar da ya yi ya saka mutane da dama sun yi alkawarin za su bashi tallafin kudade amma watanni 8 bayan babu ko daya cikinsu da ya cika alkawarin.

4. Ruqayyah Adelakin

Matashiya, Ruqayyah Adelakin, ce ta karya tarihi na shekaru 19 a Jami'ar Ladoke Akintola ta Fasaha, LAUTECH.

Ruqayyah, wacce ta kammala digiri a bangaren 'Biochemistry' ta ce da farko ba wannan makarantar ta ke son zuwa ba amma ta samu gurbin karatu kuma ta amince ta fara a maimakon zaman gida.

Waiwaye a 2021: Haziƙan Ɗaliban Najeriya 4 Da Suka Kafa Tarihin Da Ba a Taɓa Zaton Wani Zai Iya Ba
Ta karya tarihin da aka kafa shekaru 19 baya. Photo Credit: LinkedIn/Ruqayyah Adelakin
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Online view pixel