A raba mu, duka take lakaɗa min har da damƙar mazakuta na, Magidanci ya yi ƙarar matarsa Fatima

A raba mu, duka take lakaɗa min har da damƙar mazakuta na, Magidanci ya yi ƙarar matarsa Fatima

  • Wani magidanci ya garzaya kotu yana neman a raba aurensa da matarsa Fatima yana cewa ya dena kwanciyar aure da ita saboda tace yana wari
  • Har wa yau, magidancin ya kara da cewa matarsa bata ganin mutuncinsa ko na mahaifiyarsa da yan uwansa har duka take masa da damkar mazakuta
  • A bangarenta, matar, Fatima ta yi ikirarin cewa mijin ya kaurace wa shimfidarsu shekaru 3 ba dalili kuma baya kula da yaransu hudu da suka haifa

Ibadan - Wani magidanci, Olanrewaju Adeniran, a ranar Juma'a, ya fada wa kotun kwastomare da ke zamanta a Mapo, Ibadan cewa ya dena kwanciyar aure da matarsa, Fatima, domin ta ce yana wari, Daily Nigerian ta ruwaito.

Da ya ke yi wa kotun bayani, Adeniran, tsohon ma'aikacin gwamnati ya kuma nemi kotu ta datse igiyan aurensu kan cewa matarsa bata mutunta shi sannan ta fara zama barazana ga rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Kungiya Ta Yi Kira Ga 'Yan Kudancin Najeriya Su Saka Baki Don Kawo Ƙarshen Kashe-Kashe a Arewa

A raba mu, matata duka take lakaɗa min har da damƙar mazakuta na, Magidanci ya faɗa wa kotu
Magidanci ya yi karar matarsa a kotu, ya ce duka ta ke masa har da damkar mazakuta. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Bayan an daura mana aure a Mayun 1995, Fatima ta fara rashin ji. Ba ta kyautata wa mahaifiya ta da yan uwa na.
"Ta kan min duka ta damki gaba na. Fatima ta kira ni shege, malalaci da wasu sunayen da ba zan iya fada ba."

Mai shigar da karar ya kara da cewa 'yan sandan caji ofis na cocin Iyana sun kama Fatima saboda tada zaune tsaye a unguwar a shekarar 2004 kamar yadda NNN ta ruwaito.

Abin da Fatima ta shaida wa kotu

A yayin da ta ke kare kanta, Fatima ta yi ikirarin cewa mijinta ya kauracewa shimfidarsu tsawon shekaru uku ba tare da wani dalili ba.

Ta kuma yi ikirarin cewa Adeniran baya sauke nauyinsa na kulawa da yaran sa hudu.

Kara karanta wannan

Alkali ya fallasa lauyan da yayi yunkurin ba shi cin hanci a Plateau

Abin da kotu ta ce

A yayin jawabinsa, Alkalin kotun Mrs M.A. Akintayo ta gargadi ma'auratan cewa su rika takatsantsan.

Cikin bakin ciki, Akintayo ta ce Adeniran da Fatima ba su koyar da darasi mai kyau ba ga 'ya'yansu da ke kotun tare da su.

Ta bukaci bangarorin biyu su gabatar da shaidunsu sannan ta dage cigaba da zaman shariar zuwa ranar 27 ga watan Janairu domin cigaba da sauraron karar.

A raba mu, ya ce na cika mugun ci, har rufe kicin yake yi da dare, Firdausi ta yi karar mijinta Haruna a kotu

A wani labarin daban, a ranar Litinin wata Firdausi Sulaiman mai shekaru 23 ta maka mijin ta, Haruna Haruna a gaban kotun musulunci da ke zama a Magajin Gari a Kaduna tana bukatar a raba auren su da shi saboda yadda yake dukanta kamar gangar tashe sakamakon mungun cin abincin ta.

Kara karanta wannan

Gwamna ya shiga shaukin soyayya, ya zuba kalamai masu ratsa zuciya domin taya matarsa murna

Kamar yadda NewsWireNGR ta bayyana, a korafin da ta yi wa Kotu, Firdausi wacce take zama a Rigasa dake Kaduna ta ce har rufe kicin Haruna yake yi da dare.

Alkalin kotun, Nuhu Falalu, bayan sauraron bangarorin guda biyu, ya dage sauraron shari’ar har sai ranar 4 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel