Neman mafita: Lamurran tsaro sun munana, shugaban Burkina Faso ya yi murabus

Neman mafita: Lamurran tsaro sun munana, shugaban Burkina Faso ya yi murabus

  • Firaministan kasar Burkina Faso ya aje aikinsa sakamakon gazawar gwamnati wajen magance matsalar tsaro
  • A halin yanzu dai ba a kafa sabuwar gwamnati ba, amma an umarci ministoci su ci gaba da aikin kafin kafa sabuwar gwamnati
  • 'Yan Burkina Faso sun yi zanga-zangar nuna kin jinin gwamnatin, inda suka zargi gwamnati da gazawa a magance matsalolin kasar

Burkina Faso - A ranar Laraba ne gwamnatin Burkina Faso ta yi murabus bayan zanga-zangar nuna rashin amincewa da gazawarta na magance hare-haren 'yan fafutukar jihadi a kasar, Premium Times ta ruwaito.

A ranar Laraba ne firaministan kasar Burkina Faso Christophe Joseph-Marie Dabire ya gabatar da takardar murabus ga shugaban kasar Roch Marc Christian Kaboré wanda ya amince da ita.

Shugaban kasar Burkina Faso
Yanzu-Yanzu: Shugaban kasar Burkina Faso ya rushe gwamnatinsa don ayi gyara | Hoto: cgtn.com
Asali: UGC

Murabus na firaminista na nuni da kawo karshen mulkin kasar kamar yadda dokar kasar Burkina Faso ta tanada.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Ba Zan Ajiye Aiki Ba Kan Yawaitar Tserewar Fursunoni Daga Gidan Yari, Ministan Buhari

Da yake sanar da murabus din Mista Dabiré, sakatare-janar na gwamnati, Stéphane Sanou, ya karanta sanarwar shugaban kasar, yana mai cewa "an dakatar da ayyukan firaministan Mr. Dabiré," kamar yadda VON ta ruwaito.

A bisa rubutun, Mista Sanou ya ce:

"Mambobin gwamnati mai barin gado suna tabbatar da gudanar da al'amuran yau da kullum na ma'aikatun ministoci har sai an kafa sabuwar gwamnati."

Mista Dabiré ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa:

"Ina gayyatar 'yan Burkina Faso, gaba daya, da su tashi tsaye, don tallafawa shugaban Faso da sabon shugabancin da za a kafa. Ina da yakinin cewa ta hanyar hadin kai ne za mu iya tunkarar kalubalen da kasarmu da al’ummarmu ke fuskanta."

Tushen matsalolin kasar da matakai daban-daban

Makwanni da dama da suka shude 'yan kasar Burkina Faso sun nuna bacin ransu kan gazawar gwamnati wajen shawo kan matsalolin tsaro da ke addabar kasar da ke yammacin Afirka.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya yi Alla-wadai da babbaka matafiya 42 da akayi a Sokoto

'Yan adawa a ranar 9 ga Nuwamba, sun ba gwamnati wa'adin wata guda kan ta dauki "matakan gaggawa" a fuskar "tabarbarewar yanayin tsaro".

A ranar 27 ga Nuwamba, daruruwan masu zanga-zanga sun yi zanga-zanga a Ouagadougou babban birnin kasar, domin yin Allah wadai da "gazawar" gwamnati na tunkarar tashin hankalin 'yan jihadi da ke addabar kasar.

Kungiyoyin fararen hula kuma sun bukaci shugaban kasar ya yi murabus. Kimanin mutane goma ne da suka hada da yaro daya da ‘yan jarida biyu suka jikkata sakamakon tarwatsa wadannan matakai.

A ranar 14 ga Nuwamba, kasar ta shaida daya daga cikin munanan hare-hare da aka kai wa jami'an tsaronta - reshen jandarma a Inata ta Arewa.

Akalla mutane 57 da suka hada da jandarmomi 53 ne mayakan jihadi dauke da makamai suka hallaka a harin.

Tun a shekarar 2015, Burkina Faso na fama da rikice-rikicen da ake dangantawa da kungiyoyin jihadi, masu alaka da Al-Qaida da kungiyar IS.

Kara karanta wannan

Da dumi: Gwamnatin jihar Kaduna ta shirya sabon jarabawa wa Malaman makaranta 35,000

Hare-haren da ake kai wa fararen hula da sojoji na ci gaba da munana, kuma galibin hare-haren sun fi karkata ne a Arewaci da gabashin kasar. Akalla an rasa kusan mutane 2,000 yayin da miliyan 1.4 suka rasa matsugunansu.

Sheikh Gumi ya ce ba ruwansa da 'yan bindiga yanzu kam, ya fadi dalili

A wani rahoton, shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce ya daina shiga don sasantawa da ‘yan bindiga biyo bayan ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda da kotu ta yi.

Premium Times ta ruwaito cewa Gumi ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman a Kaduna a ranar Laraba 8 ga watan Disamba.

Kafin babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ayyana 'yan bindigan a matsayin ‘yan ta’adda, Gumi ya sha ziyartarsu a dazuzzukan jihohin Zamfara da Neja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel