Da Dumi-Dumi: Ba Zan Ajiye Aiki Ba Kan Yawaitar Tserewar Fursunoni Daga Gidan Yari, Ministan Buhari

Da Dumi-Dumi: Ba Zan Ajiye Aiki Ba Kan Yawaitar Tserewar Fursunoni Daga Gidan Yari, Ministan Buhari

  • Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ya ce babu dalilin da zai sa ya ajiye aikinsa kan yawaitar tserewa da fursunoni ke yi a Najeriya
  • Aregbesola ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke zantawa da manema labarai a gidan gwamnati a ranar Laraba a birnin tarayya Abuja
  • Sai dai ministan ya bawa 'yan Najeriya tabbacin cewa ma'aikatarsa za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin an kawo karshen hare-haren a gidan yarin

Abuja - Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ya ce babu wani dalili da zai sa ya ajiye aikinsa saboda yawaitar tserewa da fursunoni ke yi daga gidajen yari a sassan kasar a shekara daya da ta gabata, rahon Daily Trust.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai na gidan gwamnati baya taron mako-mako na Majalisar Kolin Kasa, FEC, da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Villa, Abuja.

Kara karanta wannan

Wani mutum ya kashe mai sayar da sigari da duka saboda N50 kacal

Da Dumi-Dumi: Ba Zan Ajiye Aiki Ba Kan Yawaitar Tserewar Fursunoni Daga Gidan Yari, Ministan Buhari
Rauf Aregbesola ya ce ba zai yi murabusa daga mukaminsa ba ka tserewar fursunoni. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu sun yi ta kiraye-kirayen cewa ya kamata ya yi murabus.

Amma, ministan wanda ma'aikatarsa ke kula da gidajen gyaran hali a dukkan kasar ya ce:

"A kan kiran cewa in yi murabus, ban ga bukatar hakan ba saboda ba rashin zama cikin shiri bane ya sa hare-haren da ake kai wa suka yi nasara, A'a."

Gwamnati za ta kara kaimi, Aregbesola

Amma, Aregbesola ya bada tabbacin cewa gwamnati za ta inganta tsaro a harabar gidajen yari duba da harin da aka kai a gidajen yarin Owerri, Oyo, Kabba da Jos cikin yan watanni da suka gabata.

A cewarsa:

"Abin da zan iya tabbatarwa yan Najeriya shine. Eh, Duk da nasarar harin da tserewar da fursunonin suka yi, muna inganta tsaro kuma ba zamu zuba ido hakan ya cigaba da faruwa ba. Wannan shine abin da ya zama dole kasa ta yi.

Kara karanta wannan

Za mu fatattaki APC daga madafun iko nan da 2023, Jerry Gana

"Muna aiki tare da dukkan bangarorin gwamnati musamman jami'an tsaro don tabbatar da cewa babu wanda zai iya balle gidajen yarin mu. Ba za mu yi kasa a gwiwa ba sai hakar mu ta cimma ruwa. Wannan shine tabbacin da muke bawa yan Najeriya."

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel