Daga Karshe: Sheikh Gumi ya ce ba ruwansa da 'yan bindiga yanzu kam, ya fadi dalili

Daga Karshe: Sheikh Gumi ya ce ba ruwansa da 'yan bindiga yanzu kam, ya fadi dalili

  • Bayan da aka yi ta cece-kuce a kansa, Sheikh Ahmad Gumi ya ce ya daina shiga tsakani kan lamarin ‘yan bindiga
  • Malamin addinin Musuluncin da ke Kaduna ya bayyana cewa ya yanke hakan ne sakamakon ayyana ‘yan bindigar a matsayin ‘yan ta’adda
  • Da wannan ayyanawar, Sheikh Gumi ya ce abu ne mai hadari a ci gaba da hada kan ‘yan bindigar da suka addabi yankin Arewa

Kaduna – Shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce ya daina shiga don sasantawa da ‘yan bindiga biyo bayan ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda da kotu ta yi.

Premium Times ta ruwaito cewa Gumi ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman a Kaduna a ranar Laraba 8 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Iyayen yara 8 da aka tsinci gawarwakinsu a wata mota sun yi martani kan lamarin

Kafin babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ayyana 'yan bindigan a matsayin ‘yan ta’adda, Gumi ya sha ziyartarsu a dazuzzukan jihohin Zamfara da Neja.

Sheikh Ahmad Mahmud Gumi
Daga Karshe: Sheikh Gumi ya ce ba ruwansa da 'yan bindiga yanzu kam, ya fadi dalili | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

A wasu lokatan, Malamin yakan yi da'awar cewa, ya kamata a tausayawa 'yan bindiga kasancewar su ma suna da 'ya'ya, kama yadda SaharaReporters ta tattaro.

Ya kuma sha yin kira ga gwamnatin tarayya da ta yi musu afuwa gaba daya kamar yadda ta yi wa tsagerun Neja Delta.

Zai zama hadari a ci gaba da shiga tsakani a lamarin 'yan bindiga, inji Gumi

Da ayyana ‘yan bindigar a matsayin ‘yan ta’adda, Gumi ya ce zai zama hadari a gare shi ya ci gaba da shiga cikin ‘yan bindigan.

Ya ce:

“Tunda gwamnatin tarayya ta ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda, ba ni da wata alaka da su kuma.

Kara karanta wannan

Shekara 1 da janye dogon yajin-aiki, akwai yiwuwar a sake rufe jami’o’i gwamnati a Najeriya

Malamin ya kara da cewa:

"Ba zan so in sanya kaina cikin hadari ba kuma in sanyawa kaina damuwa akan abin da ba dole ba.
"Na yi kokari na yi duk abin da zan iya yi don daura al'umma a kan hanya mafi kyau da ta dace a bi, amma da alama shawarata ta bi ta bayan kunne."

Sheikh Gumi ya ce zai zama "dan kallo a rikicin".

Duk da haka, ya ce yana iya sake yin duba ra'ayin nasa a nan gaba lokacin da yanayin siyasa ya canza zuwa mafi kyau.

'Yan bindiga ta'addanci kadai suke aikatawa, ba 'yan ta'adda bane, inji Gumi

A bayan dai, shahararren malamin addinin musuluncin, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce ‘yan bindiga suna aikata ta’addanci amma su ba ‘yan ta’adda ba ne.

Gumi ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Shugaban Rasha, Putin ya yi wa Gwamnatin Buhari muhimmin alkawari

Ya ce kiraye-kirayen da ake yi na gwamnati ta ayyana ’yan bindiga a matsayin ’yan ta’adda ba komai bane face rashin adalci da son zuciya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel