Shugabancin 2023: Za mu durƙusa har ƙasa don nema wa kudu maso gabas goyon bayan sauran yankuna, Ezeife

Shugabancin 2023: Za mu durƙusa har ƙasa don nema wa kudu maso gabas goyon bayan sauran yankuna, Ezeife

  • Yayin da zaben 2023 yake kara karatowa, Ibo su na ci gaba da jajircewa don neman amsar mulki ga yankin kudu maso gabashin Najeriya
  • Chukwuemeka Ezeife, tsohon gwamnan jihar Anambra ya bayyana cewa kudu maso gabas a shirye suke da su yi ko menene don neman hadin kan sauran yankuna don shugabantar kasa
  • Ya kula da yadda ‘yan kabilar Ibo su ka kawo ci gaba masu tarin yawa ga Najeriya kuma sun cancanci a kara basu damar shugabantar kasar nan

FCT, Abuja - ‘Yan kabilar Ibo su na ta ayyuka tukuru don ganin sun samu damar mulkar kasa a shekarar 2023 da ke karatowa.

Yayin da sanannu kuma manyan kasar nan su ke ci gaba da dagewa wurin ganin sun samu hadin kan sauran yankuna.

Kara karanta wannan

Zan koya wa sauran jam'iyyun siyasa mummunan darasi a 2023, gwamnan Adamawa

A ranar Asabar, 4 ga watan Disamba, tsohon gwamnan jihar Anambra, Chukwuemeka Ezeife, ya ce a shirye kudu maso gabas take da ta durkusa har kasa don neman goyon bayan sauran yankuna wurin samun damar shugabantar kasa a 2023, Premium Times ta ruwaito.

2023: Za mu iya rusuna wa da gwiwar mu mu roki goyon bayan sauran yankuna, tsohon gwamnan Anambra, Ezeife
Za mu iya rusunawa da gwiwar mu don neman goyon baya daga sauran yankuna, Ezeife. Hoto: Photo credit: Chukwuemeka Ezeife
Asali: Facebook

Ezeife ya bayyana hakan ne a wani taro na kungiyar hadin kan kasa wacce aka yi a Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Najeriya tana da damar da zata tabbatar ta tattaro kowa don a dama da shi ba tare da wariya ba.

A cewarsa:

“Na ga Hausawa, Yarabawa, Ibo da sauran kabilu a nan su na tattaunawa akan samar da shugaba na kwarai.
“Za a samu hadin kai in har aka yi adalci. Amma idan aka rasa hakan, za a samu matsala.
“Duk da Ibo ba sa durkusa wa mutane amma a wannan lokacin, a shirye muke da mu durkusa har kasa ga ko wanne dan Najeriya, ko wanne yanki da kuma ko wacce kabila.”

Kara karanta wannan

Fannin shari'ar kasar nan ba zai sassauta ba sai ya ga bayan rashawa, CJN Tanko

A cewarsa, za su durkusa kasan ne don sun yarda da kasar nan.

Ci gaban da Ibo su ka samar a yanzu haka

Ezeife ya ce Ibo sun samar da ci gaba mai tarin yawa ga kasar nan a bangaren kayan masarufi, ilimomi, sana’o’i da sauransu, don haka ya kamata ‘yan Najeriya su ba su damar shugabantar kasar.

Ya kara da cewa ya kamata a hada kai da kudu maso gabas don samun nasu gudunmawar.

Batun ba ‘yan kudu maso gabas damar shugabanci, Nkolika Mkparu, shugaban kungiyar, ta ce idan aka samar da shugaban kasa daga kudu maso gabas zai kawo hadin kai a kasar nan.

Mrs Mkparu ta ce burin kungiyarsu shi ne samar da hadin kai a harkar siyasar kasar nan.

A cewarta hakan zai kawo hadin kai don kasa ta dunkule jama’a daga yankuna daban-daban su kaunaci juna.

Rashin Adalci Ne Musulmi Ya Zama Shugaban Ƙasa Bayan Buhari, Ƙungiyar Kirista, PFN

Kara karanta wannan

Yan bindiga da Sojojin sun yi musayar wuta a Imo kan umarnin zama a gida na IPOB

A wani labarin, kungiyar Kirista ta Pentecostal Fellowship of Nigeria, PFN, ta bukaci cewa kirista ne ya dace ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari a 2023, tana mai cewa rashin adalci ne wani musulmi ya sake zama shugaba.

Shugaban PFN na kasa, Bishop Francis Wale-Oke, ne ya yi wannan kiran a karshen taron kungiyar da aka saba yi duk bayan wata hudu, da wannan karon aka yi a Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel