Annobar da ta fi Koronar farko na tunkaro duniya, kowa ya shirya inji masana

Annobar da ta fi Koronar farko na tunkaro duniya, kowa ya shirya inji masana

  • A birnin Landan, masana sun bayyana hasashen yadda annobar Korona za ta kara kamari a 'yan lokuta masu zuwa
  • Masana sun bayyana cewa, a wannan karon, annobar Korona za ta fi ta farko zafi, don haka kowa ya shirya magani
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da wani nau'in Korona mai suna Omicron ya kunno kai a duniya

Landan - Masana cututtuka, kuma daga cikin wadanda suka kirkiro riga-kafin Korona na Oxford AstraZeneca sun bayyana yadda annobar gaba da za a fuskanta a nan gaba za ta fi wacce aka sha a farkon annobar Korona.

Sun kuma shawarci duniya da ta zauna cikin shiri tare da yin koyi da darrusan da aka koya a farkon Korona domin yaki da annobar da ke dumfaro ta.

Sarah Gilbert, kwararriya a ilimin cututtuka
Wata annobar da ta fi Korona na tunkaro duniya, kowa ya shirya inji masana | bbc.com
Asali: UGC

Annaobar Korona zuwa yanzu dai ta kashe mutane miliyan 5.26 a duniya, a cewar Jami'ar Johns Hopkins yayin da ta lamushe tiriliyoyin daloli a fannin tattalin arziki kuma ta haifar da juyin rayuwa ga biliyoyin mutane.

Kara karanta wannan

Za mu fatattaki APC daga madafun iko nan da 2023, Jerry Gana

A cewar rahoton BBC, Sarah Gilbert a cikin Laccar Richard Dimbleby ta ce:

"Gaskiyar magana ita ce, na gaba zai iya zama mafi muni. Zai iya zama mafi yaduwa, ko kuma ya fi jawo mace-mace, ko duka biyun.
"Wannan ba zai kasance lokaci na karshe da kwayar cuta ke barazana ga rayukanmu da rayuwarmu ba."

Gilbert, farfesa a fannin rigakafi a Jami'ar Oxford, ta ce ya kamata duniya ta tabbatar da cewa ta yi shiri sosai don tunkarar annobar ta gaba.

A cewarta:

"Ci gaban da muka samu, da ilimin da muka samu, ba zai yiwu mu rasa su ba."

Kokarin kawo karshen cutar ta Korona dai ya ki daidaita, wanda ke da nasaba da kange damar amfani da alluran rigakafi a cikin kasashe masu karamin karfi yayin da "masu lafiya da masu arziki" a kasashe masu arziki ke samun dama, in ji masana kiwon lafiya.

Kara karanta wannan

Jerin kasashe 14 da gwamnatin Saudiyya ta haramtawa shiga kasarta saboda Korona

Wani kwamitin kwararru a kiwon lafiya da Hukumar Lafiya ta Duniya ta kafa don yin nazari kan yadda ake fama da cutar ta SARS-CoV-2 ta yi kira da a ba da tallafi na dindindin da kuma ba da damar yin bincike kan cutar ta hanyar wata sabuwar yarjejeniya.

Shawara daya ita ce ta samar da tallafin akalla dala biliyan 10 a shekara don shirye-shiryen rigakafin cutar.

An fara gano barkewar cutar ta Korona dai a kasar Sin a karshen shekarar 2019. An samar da allurar rigakafin cutar cikin kankanin lokaci.

Gilbert ta ce nau'in Korona na Omicron mai dauke da sinadarin furotin zai iya habaka yaduwar kwayar cutar, kamar yadda Reuters ta ruwaito.

A cewar Gilbert:

"Akwai karin sauye-sauye wadanda za su iya nufin kwayoyin rigakafi da alluran rigakafin suka haifar, ko kuma ta kamuwa da wasu nau'ika, na iya zama marasa tasiri wajen hana kamuwa da cutar Omicron.

Kara karanta wannan

Budurwar da ta yi karar likitar da ta bari aka haife ta ta yi nasara a kotu, za a biya ta diyyar miliyoyi

"Har zuwa lokacin da zami sami karin sani, ya kamata mu yi taka tsantsan, kuma mu dauki matakai don rage yaduwar wannan sabon nau'in."

NCDC ta bayyana dalili, ta ce cutar kwalara ta fi Korona kashe 'yan Najeriya

A wani labarin, Cibiyar Kula da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce cutar kwalara ta kashe rayuka a Najeriya fiye da yadda ake fargabar barkewar cutar Korona, musamman a shekarar 2021.

Babban Daraktan cibiyar, Ifedayo Adetifa, ya ce kasar ta sami fiye da 3,600 da suka mutu sakamakon cutar kwalara a cikin watanni 11 da suka gabata, Premium Times ta ruwaito.

A bangare guda, adadin wadanda suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Korona tun daga shekarar 2020 lokacin da ta faro a Najeriya har zuwa yanzu bai wuce 2,977.

Asali: Legit.ng

Online view pixel