NCDC ta bayyana dalili, ta ce cutar kwalara ta fi Korona kashe 'yan Najeriya

NCDC ta bayyana dalili, ta ce cutar kwalara ta fi Korona kashe 'yan Najeriya

  • Hukumar NCDC a Najeriya ta bayyana yadda cutar kwalara ke addabar 'yan Najeriya a wannan shekarar
  • Daraktan NCDC ne ya bayyana adadin mutane da suka kamu da cutar, da kuma wadanda suka mutu sakamakonta
  • Ya kuma kwatanta yadda kwalara ke da illa fiye da cutar Korona da ke addabar duniya a halin yanzu

Najeriya - Cibiyar Kula da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce cutar kwalara ta kashe rayuka a Najeriya fiye da yadda ake fargabar barkewar cutar Korona, musamman a shekarar 2021.

Babban Daraktan cibiyar, Ifedayo Adetifa, ya ce kasar ta sami fiye da 3,600 da suka mutu sakamakon cutar kwalara a cikin watanni 11 da suka gabata, Premium Times ta ruwaito.

A bangare guda, adadin wadanda suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Korona tun daga shekarar 2020 lokacin da ta faro a Najeriya har zuwa yanzu bai wuce 2,977.

Kara karanta wannan

Ranar Kanjamau ta Duniya: Mutum 35,000 na fama da cutar a jihar Kano, Gwamnatin Ganduje

Alamar cutar Korona
NCDC ta bayyana dalili, ta ce cutar kwalara ta fi Korona kashe 'yan Najeriya | Hoto: who.org
Asali: UGC

Mista Adetifa, ya bayyana haka ne yayin da yake ba da bayani game da sabon nau'in Korona na Omicron a gidan Talabijin na Channels a shirin “Sunrise Daily.”

Ya lura cewa NCDC “ta yi aiki a bayan fage don dakile yaduwar cutar kwalara, kamar yadda hankalin jama'a ya fi tafiya kan Korona fiye da sauran cututtuka."

Ya ce:

“Babu wanda ya san cewa muna da kungiyoyi a cikin jihohi biyar, shida a yanzu wadanda ke maganance kwalara. Mun sami kungiyoyi masu daukar matakin gaggawa a duk jihohin da suka sami bullar cutar kwalara.
“A halin yanzu muna shirye-shiryen lokacin cutar sankarau, duk wani horo da za a inganta, duk wani wayar da kan jama'a da za a yi sun riga sun fara aiki.

Kara karanta wannan

Ka ceto 'yan Najeriya daga yunwa da rashin tsaro, Agbekoya ga Buhari

“Don haka a bayan fage, za mu so dukkan wadannan bangarorin su samu kulawa daidai ko ma fiye da haka, amma ba mu da wani zabi illa mu mayar da hankali kan dukkan cututukan da ka iya yin illa ga lafiyar al’umma a kasar nan kamar yadda umarnin da muka samu ya nuna."

Da yake karin haske, Mista Adetifa ya ce an samu bullar cutar kwalara a jihohi daban-daban a lokuta daban-daban, yana mai cewa wasu daga cikin jihohin an samu gajeriyar bullar cutar, yayin da wasu kuma suka dade ana samun bullar cutar.

Ya kuma bayyana cewa ruwan sama da ake samu a wuraren da ake ba haya sakaka sun fi fuskantar barazanar kamuwa da cutar kwalara, inda ya danganta samuwar kwalara da lokacin damina.

Ya kuma bukaci hukumomin jihohi da su saka hannun jari a harkar ruwa da tsaftar muhalli a fadin tarayyar kasar nan.

Kwalara da Korona

Kara karanta wannan

Yawan 'yan Najeriya na bamu tsoro, dole mu yi wani abu, inji gwamnatin Buhari

Ya zuwa ranar 21 ga Nuwamba, 2021, NCDC ta bayyana cewa Najeriya ta sami adadin mutuwar mutane 3,566 da kuma 103,589 da ake zargin sun kamu da cutar kwalara a cikin jihohi 32 na tarayya da kuma FCT.

A cewar cibiyar, jihohi hudu - Bauchi (19,470), Jigawa (13,293) Kano (12,116), Zamfara (11.918) sun dauki kashi 55$% cikin 100% na dukkan wadanda suka kamu da cutar.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar sun nuna cewa adadin wadanda suka kamu da cutar Korona a Najeriya ya kai 2,977, yayin da adadin wadanda suka kamu da cutar ya karu zuwa 214,218 a ranar Talata, bayan an tabbatar da kamuwar mutane 105.

Kasar Kanada ta sa takunkumi ga 'yan Najeriya saboda bullar Korona

A jiya Laraba, kasar Kanada ta sanya dokar hana shigar yan Najeriya kasar a wani yunkuri na dakile yaduwar nau'in cutar Korona na Omicron, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yan bindiga da Sojojin sun yi musayar wuta a Imo kan umarnin zama a gida na IPOB

Kasar ta Arewacin Amurka da ke samun kwararar bakin haure daga Najeriya ta sanar da hakan ne a safiyar yau Laraba 1 ga watan Disamba.

Ya zuwa yanzu, hukumomin Kanada sun haramtawa kasashe 10 shiga kasarsu saboda bullar sabon nau'in na Korona.

Asali: Legit.ng

Online view pixel