Za mu fatattaki APC daga madafun iko nan da 2023, Jerry Gana

Za mu fatattaki APC daga madafun iko nan da 2023, Jerry Gana

  • Farfesa Jerry Gana, tsohon ministan yada labarai na Najeriya, ya ce za su fatattaki jam'iyyar APC daga mulki a zabe na gaba
  • Gana ya ce munafukai sun cika madafun iko karkashin jam'iyya mai mulki inda ya jaddada cewa akwai bukatar kawo sauyi
  • Kamar yadda Gana ya ce, dole matasa su kasance masu gaskiya da rikon amana domin shi ne tushen shugabanci nagari
  • A taron matasa na wannan shekarar, Gana ya ce ba haifar shugabanni nagari ake yi ba, rainon su ake yi domin gobe

Tsohon ministan yada labarai da wayar da kai, Farfesa Jerrry Gana, ya ce sai sun fatattaki jam'iyya mai mulki ta APC tare da korar ta daga madafun iko a shekarar 2023.

Gana ya tabbatar da cewa, jam'iyyar mai mulki ta aikata manyan laifuka na rashin adalci ga jama'a kuma 'yan Najeriya sun gaji da mulkinta, Thisdaylive ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Matasan Najeriya ba su shirya karbar shugabanci ba, Mamban APC

Gana ya sanar da abinda ke zuciyarsa ne a ranakun karshen mako a Effurun, kusa da warri inda ya yi wata lakca mai taken “Raising 21st Century Leaders for Nigeria” a wani taron matasa na 2021.

Za mu fatattaki APC daga madafun iko nan da 2023, Jerry Gana
Za mu fatattaki APC daga madafun iko nan da 2023, Jerry Gana. Hoto daga thisdaylive.com
Asali: UGC

Ya jajanta cewa, akwai munafukai masu tarin yawa a madafun ikon kasar nan kuma ya jaddada cewa akwai bukatar kawo canji domin cigaban kasar nan, ThisDay ta ruwaito.

Tsohon ministan ya yi kira ga matasan Najeriya da su koyi dabi'ar gaskiya da rikon amana a duk abinda za su yi domin gaskiya da rikon amana ce tushen shugabanci nagari.

Ya kalubalanci matasa da su mayar da hankalinsu wurin siyasa da shugabanci nagari kuma ya shawarce su da su saba da mutunta juna da kuma zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Bayan Twitter, gwamnatin Buhari za ta sanya wasu ka'idoji kan NETFLIX da sauransu

"Ku kasance masu gaskiya da kuma fadin gaskiya a kodayaushe. Gaskiya ita ce mabudin kowanne ilimi. Za ta iya fitar da al'umma daga halin kunci. Shugabanni nagari ba bayyana suke ba, rainon su ake yi. Ya dace mu jinjina wa shugabanni nagari, ku zama shugabanni nagari," yace.

Matasan Najeriya ba su shirya karbar shugabanci ba, Mamban APC

A wani labari na daban, mamba a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Ribas, Karibi Bob Manuel, ya ce matasan Najeriya ba su da ra'ayin bibiyar shugabanninsu domin karbar shugabanci.

Bob Manuel ya sanar da kamfanin daillancin labaran Najeriya a Fatakwal jihar Ribas a ranar Juma'a cewa, yanayin yadda matasa ke martani kan manyan abubuwan da ke faruwa a kasar nan ne ya nuna hakan, Daily Trust ta ruwaito.

"Muna cikin wani hali wanda matasa suke nuna kamar komai daidai tare da sakarcin bibiyar shugabannin siyasa ba tare da wani tunani ba.

Kara karanta wannan

Zan koya wa sauran jam'iyyun siyasa mummunan darasi a 2023, gwamnan Adamawa

"Matasa suna yi kamar wasu wadanda aka siya ko kuma marasa alkibla wadanda a koyaushe ake juya mu son rai tamkar sakako kuma ake nuna mana abinda ya dace mu yi," ya jajanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel