Budurwar da ta yi karar likitar da ta bari aka haife ta ta yi nasara a kotu, za a biya ta diyyar miliyoyi

Budurwar da ta yi karar likitar da ta bari aka haife ta ta yi nasara a kotu, za a biya ta diyyar miliyoyi

  • Evie Tombes, wata mata yar kasar Burtaniya da ta yi karar likitan mahaifiyarta a kotu kan dalilin da yasa ta bari aka haife ta ta yi nasara
  • Evie ta yi ikirarin cewa likitan bata bawa mahaifiyarta shawarar shan wasu magunguna ba kafin a dauki cikinta
  • Sakamakon rashin shan magungunan, an haife Evie da wata cuta mai wadda har tsawon rayuwanta za ta rika shan magunguna

Burtaniya - Matar da ta yi karar likitan mahaifiyarta a kotu saboda ta bari an haife ta za ta samu miliyoyi a matsayin diyya, Times Now ta ruwaito.

Evie Tombes ta yi karar likitan mahaifiyarta ne kan 'kuskure yayin daukan ciki' don an haife ta da wani cuta da ake kira spina bifida a 2001.

Cutar da ba a cika samunsa ba yana shafar kashin baya ne kuma wasu lokutan yana nakasar da mutum har abada. Hakan yasa Evie a duk rayuwarta sai an jona mata robobi na magani.

Kara karanta wannan

A cikin shekaru 3, motoci 30 na sata, Wanda ake zargi da fashi da makami

Budurwar da ta yi karar likitar da ta bari aka haife ta ta yi nasara a kotu, za a biya ta diyyar miliyoyi
A biya ta diyya, Budurwar da ta yi karar likitar da ta bari aka haife ta ta yi nasara a kotu. Hoto: Daily Mail
Asali: UGC

Har karshen rayuwar Evie za ta rika shan magunguna

Economic Times ta rahoto cewa Evie za ta samu matsaloli na motsawa a nan gaba hakan na nufin za ta shafe mafi yawan rayuwarta ne a kujeran guragu sannan za ta samu matsalar bayan gida da koda.

Matashiyar mai shekaru 20, tana fafatawa a wasar tsallen doki da mutane masu nakasa har ma da masu lafiya, ta yi ikirarin cewa likitan, Dr Philips bata fada wa mahaifyarta ta rika shan sinadarai masu gina jiki ba kafin ta dauki cikinta.

Kotu ta goyi bayan Evie

Mai Shari'a Rosalin Coe QC ta goyi bayan Evie a yayin yanke hukunci a wata Babban Kotun Landan a ranar Laraba.

Alkalin ta ce idan da an bawa mahaifiyar Evie shawarwarin da suka dace, da ta jinkirta daukan cikin.

Kara karanta wannan

BaAmurkiya mai digiri 4 ta gangaro Afrika, ta yi wuff da dan achaba, tace hadin Ubangiji ne

Lauyoyin Evie sun ce a halin yanzu ba a gama lissafa adadin kudin diyyar da za a biya ta ba amma sun ce kudi mai mai yawa domin tana bukatar kudaden da za ta kula da lafiyarta.

Evie ta gana da yan gidan sarautan Ingila, Yarima Harry da Megan Markle a shekarar 2018 a lokacin da ta lashe wata kyauta ta yara a taro da Well Child ta shirya.

Da baki bari an haifeni ba: Budurwa ta shigar da Likitar da ta karbi haihuwarta kotu

Tunda farko, budurwar mai suna Evie Toombes, mai cutar Spina Bifida, ta kai karar Likitarta da kula da mahaifiyarta lokacin da take dauke da cikinta shekaru 20 da suka gabata.

A cewarta, Likitar ta ki baiwa mahaifiyarta shawara ta sha wasu magunguna da ka iya kawar da cutar lokacin da take cikin mahaifa, rahoton Dail Mail.

Mahaifar mai suna Caroline, mai shekaru 50 yanzu ta ce lokacin da ta tuntubi Likitar a 2001 kuma sukayi magana kan Folic Acid, bata fada mata shan maganin zai hana jaririyarta kamuwa da cutar spina bifida ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel