Babbar magana: Yadda wani mutumi ya sayi mataccen gida kan kudi N416m ta yanar gizo

Babbar magana: Yadda wani mutumi ya sayi mataccen gida kan kudi N416m ta yanar gizo

  • Wani mutum ya bada mamaki yayin da ya siya wani gida da aka yi watsi da shi mai shekaru 400 wanda aka bayyana a matsayin hatsari ga mai saye
  • Gidan wanda aka saya ta yanar gizo akan kudi fam 760,000 (N416 miliyan) an ce a cikinsa akwai tarin beraye, zomaye da jabaye kuma zai bukaci gyara mai yawa
  • Wani abin sha'awa, an yi gwanjon gidan wanda ya kunshi dakuna guda uku, kicin da dakin ajiya ba tare da nuna ya cikinsa yake ba

Kamar dai abin da wasu ba za su iya fahimta ba, wani mutum da ba a san ko wanene ba ya yi abin da ba kowa ne zai iya yi ba.

Jaridar Mirror ta rawaito cewa wani mutum ya sayi wani gidan da aka yi watsi da shi mai shekaru 400 wanda aka bayyana a matsayin gida mai hatsarin gaske akan kudi Fam 760,000 (kwatankwacin N416m).

Kara karanta wannan

BaAmurkiya mai digiri 4 ta gangaro Afrika, ta yi wuff da dan achaba, tace hadin Ubangiji ne

Hotunan gidan da aka siya da tsada
Yadda wani mutum ya sayi mataccen gida a kudi N416m a kasar waje | Hoto: Daily Mail
Asali: UGC

Gidan Elizabeth Cottage da ke Burtaniya an ce yana cike da zomaye, beraye da jabaye kuma yana bukatar gyara gaba dayansa idan ana so ya dawo cikin siffarsa mai kyau.

Yaya munin gidan yake?

Da yake ba da karin bayani kan yanayin lalacewar gidan da aka siyar ta hanyar gwanjon kai tsaye a kafar intanet, Daily Mail ta bayyana cewa benayensa ba su da kyau kuma yana iya rushewa a kowane lokaci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Crookham Common, gidan da Brighton Auction House Sussex ya yi gwanjonsa an ce tsabar muninsa da lalacewarsa, ba za a iya daukar hoton cikinsa ba, saboda tsoron kada ya rushe.

Lambun gidan an ce akwai zomaye, beraye da jabaye da yawa, da ma yiwuwar a samu wasu dabbobin da ba a sani ba.

Gidan mai dakuna 4 ne

Kamfanin gwanjon ya bayyana cewa gidan mai dauke da dakuna 4. Yana da dakuna 3 da bandaki 2 a benen sa na farko.

Kara karanta wannan

Hamshakin mai kudi ya gina gidaje 90, ya bada kyautarsu a murnar bikin diyar shi

Babban bangarensa ya kunshi dakunan liyafa 3, kicin/dakin karin kumallo da dakin ajiya.

Wata sanarwa da ke bayyana yadda cikin gidan yake tana cewa:

"Damar da ba a saba gani ba ta siyan katafaren gida mai dakuna hudu akan kyakkyawan fili a yankin karkara, yana bukatar cikakken gyara.
“Gidan bai da kyau kuma ga alama an yi watsi dashi na tsawon shekaru da yawa. Elizabeth Cottage da filinsa na nan a kan wani fili mai girman eka 1.5, tare da samun isa ga Crookham Common ta baya.
''A kasa akwai dakuna uku da bandaki biyu. A bayan gidan, akwai katafaren gida mai daki daya da waje."

Ra'ayi: Bidiyon matashin da ya bar sana'a ya koma zama don kallon jiragen kasa

A wani labarin, wani matashi mai suna Francis Bourgeois ya jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta bayan da ya bayyana a shafukansa na sada zumunta cewa ya bar sana'arsa.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya bayyana yadda 'yan bindiga suka fi gwamnati son ganin karshen ta'addanci

Matashin ya ce yanzu yana so ya yi amfani da cikakken lokacinsa ne kawai don ganin wucewar jiragen kasa. A halin yanzu babu wanda ya san ko zai sami wani aikin a gefe don biyan bukatunsa.

Da ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Instagram, matashin ya rubuta cewa:

"Yau na bar aikina don yin aikin kallon jiragen kasa na cikakken lokaci na!"

Asali: Legit.ng

Online view pixel