Da Dumi-Dumi: Shugaban kamfanin Twitter, Jack Dorsey, ya yi murabus daga mukaminsa

Da Dumi-Dumi: Shugaban kamfanin Twitter, Jack Dorsey, ya yi murabus daga mukaminsa

  • Shugaban kamfanin sada zumunta Tuwita, Jack Dorsey, ya yi murabus daga mukaminsa ranar Litinin
  • Shugaban mai barin gado, shine ya kirkiri kamfanin a shekarar 2006, kuma ya sanar da wanda zai maye gurbinsa
  • Sabon shugaba Parag Agrawal, ya fara aiki da kamfanin ne a shekarar 2011, kuma shike jagorantar sashin fasaha

Jaridar Dailytrust ta rahoto cewa shugaban kamfanin Tuwita, Jack Dorsey, ya yi murabus daga kan mukaminsa.

Dorsey ɗan kimanin shekara 45 a duniya, shine ya kirkiri kamfanin na Tuwita a shekarar 2006, kuma ya sanar da murabus ɗinsa ne a wani rubutu da ya wallafa ranar Litinin.

A rubutun Dorsey ya bayyana cewa, "Daga karshe lokaci ya yi da zan matsa gefe," inda ya kuma kara da cewa, "na ɗauki wannan matakin ne saboda na yi imanin cewa kamfanin zai ci gaba da gudana a hannun wanda zai gaje ni."

Kara karanta wannan

Innalillahi: Wani Lakcara ya yanke jiki ya faɗi ana tsaka da taro, ya rigamu gidan gaskiya

Jack Dorsey
Da Dumi-Dumi: Shugaban kamfanin Twitter, Jack Dorsey, ya yi murabus daga mukaminsa Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Waye zai maye gurbinsa?

Tsohon shugaban kamfanin ya sanar da Parag Agrawal, tsohon shugaban sashin fasaha na kamfanin, a matsayin wanda zai maye gurbinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dorsey ya kara da cewa ya amince sosai da basirar wanda zai gaji mukaminsa na shugaba, tare da masa fatan alheri, yace, "lokaci ya yi da zai zo ya shugabanci kamfanin."

Sabon shugaba ya yi jawabi

A wani rubutu da ya buga a dandalin na Tuwita, Agrawal ya gode wa shugaba mai barin gado Jack da kuma kamfanin Tuwita bisa amince masa da suka yi.

Sabon shugaban yace:

"Ina mika tsantsar godiya ta ga Jack Dorsey da tawagar kamfanin Tuwita baki ɗaya, fatan nasara gare mu nan gaba."
"Ina kara gode wa kamfanin Tuwita bisa amincewa da ni da bani goyon baya na maye gurbin shugaba."

BBC Hausa ta rahoto cewa Agrawal ya fara aiki da kamfanin Tuwita ne a shekarar 2011, kuma ya kasance shugaban sashin fasaha na kamfanin tun daga 2017.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya bayyana yadda 'yan bindiga suka fi gwamnati son ganin karshen ta'addanci

A wani labarin na daban kuma Minista ya fadi abin da ya hana Twitter ya dawo aiki a Najeriya Wata 1 bayan Buhari ya yi alkawari

Karamin Ministan kwadago da samar da ayyukan yi na kasa, Festus Keyamo, yace har yanzu gwamnatin Najeriya ta na tattaunawa da Tuwita.

Keyamo SAN yace zaman gwamnatin tarayya da kamfanin yana tafiya, kuma sharuda kadan suka rage a ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel