Wata 1 bayan Buhari ya yi alkawari, Minista ya fadi abin da ya hana Twitter ya dawo aiki

Wata 1 bayan Buhari ya yi alkawari, Minista ya fadi abin da ya hana Twitter ya dawo aiki

  • Festus Keyamo SAN ya bayyana inda aka kwana a kan batun haramta amfani da Twitter a Najeriya
  • Ministan kwadago da samar da ayyukan yace Twitter sun amince da sharudan da aka gindaya masu
  • Keyamo SAN yace ana jiran lokaci ne kawai domin a kyale mutane su cigaba da amfani da Twitter

Abuja - Karamin Ministan kwadago da samar da ayyukan yi na kasa, Festus Keyamo, yace har yanzu gwamnatin Najeriya ta na tattaunawa da Twitter.

Jaridar Premium Times ta rahoto Festus Keyamo SAN yana cewa zaman gwamnatin tarayya da kamfanin yana tafiya, kuma sharuda kadan suka rage a ciki.

Da yake bayani a kan batun kwanakin baya, Keyamo ya yi alkawarin gwamnatin Muhammadu Buhari za ta cire takunkumin da ta sa wa kamfanin Twitter.

Ministan yace kamfanin kasar wajen ya kusa cika duka sharudan da aka sa masa kafin ya dawo aiki a Najeriya tun bayan dakatar da su a farkon watan Yuni.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya bayyana yadda 'yan bindiga suka fi gwamnati son ganin karshen ta'addanci

A cewar Keyamo, kamfanin ne ya nemi ya yi sulhu da gwamnati. Daga nan aka ba su jerin wasu sharudodi da za su cika, sannan suka ce duk sun ji, sun gani.

Buhari
Shugaban Najeriya Hoto: @bashahmad
Asali: Facebook

Ina aka kwana?

“Twitter ne suka tuntubi gwamnatin tarayya, suka ce su na son sanin yadda za su karfafa alakarsu da gwamnati, kuma sun yi nisa a kan wannan.”
“Amma mun bar sharudodi da yawa, kuma sun amince da sharudan. Abin da ya rage yanzu shi ne tsawon wa’adin da za a cika sharudan.” – Keyamo.
“Da zarar lokacin ya yi, sun cika wadannan sharuda, Twitter zai dawo bakin aiki a Najeriya. Sun san abin da mu ke so. Kuma babu son kai a sharudan.”

Twitter sun cika sharuda - FG

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga sun tayar da wani ƙauye bayan sun yi wa mutum 7 kisar gilla

The Nation tace daga cikin sharudan da aka ba Twitter shi ne za su rika biyan haraji ga gwamnati, sannan za su bude ofishin da mutane za su kai kuka.

Keyamo wanda yana cikin kwamitin da ke zama da Twitter yace bai dace a kyale mutane su yi amfani da Twitter, su yi abin da zai jawo tashin-tashin a kasa ba.

“Sun yarda da biyan haraji da bude ofis a Najeriya. Akwai inda bai kamata mutane su shiga ba, ko su rika daura abubuwan da za su raba kanmu.” – Keyamo.

Wata 1 bayan Buhari

Kwanaki aka ji Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurnin a dage daktarwar da aka yi wa Twitter.

A jawabinsa na samun 'yancin-kai, shugaban kasar ya ce kwamitin da ya kafa ta tattauna da Twitter sun cin ma matsaya, amma yanzu kamfanin bai dawo aiki ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel