Innalillahi: Wani Lakcara ya yanke jiki ya faɗi ana tsaka da taro, ya rigamu gidan gaskiya

Innalillahi: Wani Lakcara ya yanke jiki ya faɗi ana tsaka da taro, ya rigamu gidan gaskiya

  • Wani malami a kwalejin fasaha dake Offa jihar Kwara, Ayatu Ikani, ya yanke jiki ya faɗi, kuma ya rasa rayuwarsa daga faruwar haka
  • Rahotanni sun bayyana cewa Ayatu na cikin gudanar da taro da mutanensa, yayin da lamarin ya faru da shi
  • Shugaban sashin yaɗa labarai na wurin aikin marigayin, yace za'a yi jana'izarsa a mahaifarsa ranar Talata

Kwara - Wani malami a kwalejin fasaha dake Offa, jihar Kwara, Mista Ayatu Ikani, ya rigamu gidan gaskiya.

Jaridar Dailytrust ta rahoto cewa Mista Ayatu ya yanke jiki ya faɗi yayin da suke cikin taro da mutanensa a Offa, jihar Kwara.

Duk wani kokari da mutanen yankinsa za su yi na ganin ya farfarɗo, sun yi amma ba su samu nasara ba saboda lokacinsa ya yi.

Jihar Kwara
Innalillahi: Wani Lakcara ya yanke jiki ya faɗi ana tsaka da taro, ya rigamu gidan gaskiya Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Kafin rasuwarsa, Ayatu ɗan asalin jihar Kogi ne, kuma babban malami ne a sashin koyar da aikin jarida na kwalejin fasaha dake Offa.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Dan majalisar dokoki na jam'iyyar APC ya riga mu gidan gaskiya

Kazalika marigayin shine sakataren yankin Igala dake karamar hukumar Offa a jihar ta Kwara.

Wani majiya ya bayyana mamacin da mai kulawa da addininsa yayin da ya halarci sallar Jumu'a, kuma malami ne nagari mai aiki tukuru.

Mutumin ya kara da cewa a halin yanzun an kai gawarsa dakin aje gawarwaki na babban asibitin Offa.

Kwalejin fasaha ta tabbatar da mutuwarsa

Shugaban sashin yaɗa labarai na kwalejin, Olayinka Iroye, ya tabbatar da rasuwar malamin dake aiki a makarantar su.

Ya kuma bayyana cewa za'a gudanar da jana'izarsa a garin da aka haife shi, dake karamar hukumar Ofu, jihar Kogi, ranar Talata.

Iroye yace:

"Mista Ayatu na aiki a sashin koyar da aikin sadarwa da bayanan fasaha na kwalejin kuma ya rike mukamai da dama."
"Daga cikin mukaman da ya taba rike wa akwai jami'in kula da harkokin jarabawa, da dai sauran su."

Kara karanta wannan

Dan shekara 78 ya kashe dan'uwansa mai shekaru 94 kan rikicin fili a Ondo

A wani labarin na daban kuma Dalibar Jami'ar BUK ta mutu tana tsaka da Sallah a dakin kwanan dalibai

Wata daliba dake ajin karshe a jami'ar Bayero dake Kano ta rasa rayuwarta a ɗakin kwanan ɗalibai bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

Rahotanni sun bayyana cewa, Binta Isa, ta faɗa wa abokan zaman ta a ɗaki cewa tana jin ciwan kirji, tana fara sallah ta rasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel