Tsohon limamin Ka'aba, Sheikh Adil Al-Kalbani ya zama jarumin fina-finai

Tsohon limamin Ka'aba, Sheikh Adil Al-Kalbani ya zama jarumin fina-finai

  • Tsohon limamin Ka'aba, Sheikh Adil Al-Kalbani, ya bayyana a wani gajeriyar tallar wani fim mai suna Combat Zone
  • Bayan wallafa bidiyon a Twitter, Sheikh Al-Kalbani ya je kasa inda yayi tsokacin cewa, kuna ganin zan iya kasuwa a Hollywoood?
  • Wannan al'amarin ya tashi hankalin jama'a inda aka dinga masa tsokaci tare da fatan samun shiriyar Allah gare shi

A wani bidiyo mai tsawon minti biyu da dakika arrba'in da daya, tsohon limamin Ka'aba, Sheikh Adil Al-Kalbani ya bayar da cikakken gabatarwa na matsayinsa.

Kamar yadda The Islamic Information suka ruwaito, Fim din mai suna Combat Zone, ya shahar tunda tsohon limamin Kaaba Imam Sheikh Adil bin Salem bin Saeed Al-Kalbani da wasu 'yan kwallon kafa ne suke tallarsa.

Tsohon limamin Ka'aba, Sheikh Adil Al-Kalbani ya zama jarumin fina-finai
Tsohon limamin Ka'aba, Sheikh Adil Al-Kalbani ya zama jarumin fina-finai. Hoto daga theislamicinformation.com
Asali: UGC

Wannan sabon al'amarin kuwa ya janyo cece-kuce tare da maganganu a kafafen sada zumuntar zamani, The Islamic Information suka ruwaito.

Kara karanta wannan

Labari da duminsa: Tsohon sanatan APC ya yanki jiki ya fadi, ya rigamu gidan gaskiya

Sheikh Adil Al-Kalbani ya bayyana a wani bidiyo na talla wanda ke bayyana sojoji suna yaki kuma suna amfani da makamai. A cikin gajeren bidiyon, an ga limamin Ka'aban ya na bayani dalla-dalla.

Hukumar kula da nishadi ta kasar Saudi Arabia ce ta wallafa bidiyon a shafin Turki al-Sheikh na Twitter.

A kasan wannan wallafar, tsohon limamin Ka'aban, Sheikh Adil Al-Kalbani ya je cike da ba a inda ya wallafa, "Kuna tunanin zan iya zuwa masana'antar fina-finai ta turawa?" a kasan bidiyon da aka wallafa.

Ma'abota amfani da kafafen sada zumunta sun caccaki Sheikh Al-Kalbani bayan ya bayyana a bidiyon.

Wani ya ce a gaskiya ganin shi a bidiyon ya zama banbarakwai, wani kuma martani yayi da cewa, "Allah ya shiryar da kai kuma ya bude maka zuciya."

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsohon kwamishinan jihar Delta, Kenneth Okpara ya mutu

Jarumar mata: Kamala Harris ta zama mace ta farko da ta zama shugaban kasar Amurka

A wani labari na daban, mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Kamala Harris ta kafa tarihi a yayin da ta zama mace ta farko a duniya da ta samu karfin ikon shugabancin kasar Amurka yayin da shugaban kasa Joe Biden ya tafi asibiti.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, a wata takarda da Jen Psaki, sakataren fadar shugaban kasan ya fitar, yace Joe Biden zai je asibiti ne domin duba lafiyarsa.

"Mataimakiyar shugaban kasan za ta dinga aiki daga ofishin ta da ke West Wing a cikin wannan lokacin."

Asali: Legit.ng

Online view pixel