Da dumi-dumi: Tsohon kwamishinan jihar Delta, Kenneth Okpara ya mutu

Da dumi-dumi: Tsohon kwamishinan jihar Delta, Kenneth Okpara ya mutu

  • Kenneth Okpara, tsohon kwamishinan tattalin arziki na jihar Delta ya mutu
  • Okpara mai neman takarar kujerar gwamnan jihar a zaben 2023 ya mutu a safiyar Juma’a, 19 ga watan Nuwamba
  • Ya shafe tsawon shekaru uku yana fama da rashin lafiyar da ba a sani ba

Tsohon kwamishinan tsare-tsaren tattalin arziki da kudi kuma mai neman takarar gwamnan jihar Delta a zaben 2023, Kenneth Okpara ya mutu.

An haifi Okpara a ranar 8 ga watan Fabrairu, 1961, ya kuma fito daga masarautar Eku, karamar hukumar Ethiope East na jihar Delta.

Da dumi-dumi: Tsohon kwamishinan jihar Delta, Kenneth Okpara ya mutu
Da dumi-dumi: Tsohon kwamishinan jihar Delta, Kenneth Okpara ya mutu Hoto: Delta state government
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan jihar, Emmanuel Iduaghan ne ya nada shi a matsayin kwamishinan tattalin arziki daga Satumban 2011 zuwa Yulin 2013.

Ya kuma kasance kwamishinan kudi daga Yulin 2013 zuwa Mayun 2015.

Kara karanta wannan

Rahoto: Yadda aka hallaka mutane 52 a Sokoto cikin kwanaki biyu kacal

Okpara, wanda ya kasance dan jam’iyyar PDP ya yi fama da wata rashin lafiya da ba a sani ba tsawon shekaru uku.

Ya mutu a safiyar Juma’a, 19 ga watan Nuwamba, a wani asibiti da ba a bayyana ba, Sahara Reporters ta rahoto.

A daidai lokacin kawo wannan bayani, babu cikakken bayani kan mutuwar Okpara amma wani jami’i da ya nemi a boye sunansa ya tabbatar da mutuwar nasa.

Jami’in na PDP ya ce:

“Eh Kenneth Okpara ya mutu, ya mutu da misalin karfe 4:00 na asuba kuma shikenan abun da zan iya fadi. Allah ya ji kansa amin.”

PM News reports that the international financial expert and astute political leader died in the oil-rich city of Warri. Read more: https://www.legit.ng/politics/1444223-breaking-delta-state-commissioner-kenneth-okpara-dead/

Kara karanta wannan

Har bayan wata 7, an kasa sasanta rikicin Kwankwaso da Wali a PDP

PM News ta ruwaito cewa kwararren kan harkokin kudi kuma hazikin dan siyasan ya mutu a birnin Warri.

Dan uwan Hamshakin Attajiri a nahiyar Afirka, Aliko Dangote, ya rigamu gidan gaskiya

A wani labarin, mun kawo a baya cewa mataimakin shugaban kamfanin Dangode Group kuma ɗan uwa ga Attajirin Afirka, Aliko Dangode, Sani Dangote, ya riga mu gidan gaskiya.

Rahotanni sun bayyana cewa Sani Dangote ya rasa rayuwarsa ne bayan fama da jinya a kasar Amurka ranar Lahadi.

Wannan na kunshe ne a wani gajeren sako da rukunin kamfanonin Dangote, Dangote Industries, suka buga a shafinsu na Facebook.

Asali: Legit.ng

Online view pixel