Labari mai dadi: FG ta na kokarin karairaya farashin kayan abinci, Ministan noma

Labari mai dadi: FG ta na kokarin karairaya farashin kayan abinci, Ministan noma

  • Ministan harkokin noma da habaka karkara, Mohammed Abubakar, ya ce gwamnatin tarayya ta na kokarin karya farashin kayan abinci
  • Kamar yadda sabon ministan ya bayyana a Abuja, Buhari ya na da burin ganin talaka bai rasa abinci ba kuma ana noma shi a kasar nan
  • Ya sanar da kokarin da gwamnati ta ke yi wurin ganin tallafin noma ya isa kai tsaye ga manoma ba tare da ya bi ta hannun wasu ba

Abuja - Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta na yin duk abinda ya dace wurin ganin ta ragargaza farashin kayan abinci a kasar.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ministan ayyukan noma da habaka karkara, Mohammed Abubakar, ya sanar da hakan a Abuja yayin wata tafiyar gane juna da yayi a hukumar binciken aikin noma ta Najeriya.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Dalibin da ya lakadawa lakcararsa duka ya bayyana dalilin dukanta

Labari mai dadi: FG ta na kokarin karairaya farashin kayan abinda, Ministan noma
Labari mai dadi: FG ta na kokarin karairaya farashin kayan abinda, Ministan noma. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya na da matukar son noma da kiwo kuma ya mayar da hankali wurin ganin cewa mutane su na da "abincin da za su ci a kowacce rana ba tare da sun wahala ba."

Ministan yace: "Muna iyakar bakin kokarinmu wurin ganin mun samo wasu hanyoyin da za su karya farashin kayan abinci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A gaskiya, babu wanda zai zauna ya na kallo. Muna yin duk abinda ya dace wurin ganin cewa mun inganta fannin noma da kiwo kuma abincin da dukkan kasar Najeriya za ta ci ana samar da shi a cikin gida, hakazalika naman da ake amfani da shi."

Ya ce Buhari ya bada umarnin bada kula ta musamman ga cibiyoyin bincike na fadin kasar nan kuma hakan ya bai wa fifiko domin ganin an habaka hanyoyin samar da abinci, Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda wani mutum ya hargitsa zaman lafiyar banki kan batun BVN

ya ce gwamnati ta shirya wurin sake gabatar da tsarin Growth Enhancement Scheme (GES), shekaru kalilan bayan an kankare shi.

"Babban abinda ya fi damu na shi ne ganin yadda kayan tallafi za su iska manoma kai tsaye ba tare da wasu sun rike ba. Za mu yi duk abinda ya dace wurin ganin asalin manoman sun samu tallafin da ya dace," yace.

Shugaban BUA: Kawo kwantena daga China zuwa Legas ya fi arha kan kai ta daga Legas zuwa Kano

A wani labari na daban, Abdussamad Rabiu, shugaba kuma mamallakin kamfanin BUA, ya ce ya fi arha a dauko kwantena daga China zuwa Legas a kan daga Legas zuwa Kano.

Ya sanar da hakan ne a birnin Paris yayin da ya ke tsokaci a kan damammakin da akwai a fannin sufurin Najeriya, ballantana a fannin jiragen ƙasa, Daily Trust ta wallafa.

Rabiu ya ce saka hannun jari ballantana a fannin jiragen ƙasa zai samar da damammaki ga ƙasar da masu saka hannayen jarin.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro, ambaliya da dalilai 4 da suka jawo tsada da hauhawan farashin abinci

Asali: Legit.ng

Online view pixel