Pantami, Dangote da wasu jiga-jigai da suka yi Umrah tare da Buhari a Makkah

Pantami, Dangote da wasu jiga-jigai da suka yi Umrah tare da Buhari a Makkah

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gudanar da aikin Umrah a kasar Saudiyya tare da tawagarsa
  • Shugaban ya samu rakiyar manya na kusa dashi a gudanar da mulkin kasar, ciki har da minista Pantami
  • Hakazalika, Dangote da wasu manyan 'yan kasuwa su ma sun halarci ibadar ta Umarah, inda suka yi wa kasa addu'a

Makkah, Saudiyya - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi nasarar gudanar da aikin Umrah a babban masallacin Makkah na kasar Saudiyya tare da ministan sadarwa Isa Pantami da ’yan kasuwa Aliko Dangote da Abdulsamad Rabiu da Dahiru Mangal da Wale Tinubu, The Nation ta ruwaito.

Umrah dai ibada ce mai matukar muhimmanci ga al'ummar musulmi. An yi imani da cewa dukkan bukatun da aka roki Allah a yayin gudanar da aikin, Allah yana amsa su.

Read also

Labarin Hotuna: Dangote, AbdulSamad, Mangal, Shugaba Buhari sun gudanar da aikin Umrah

Pantami, Dangote da wasu jiga-jigai da suka yi Umrah tare da Buhari a Makkah
Shugaba Buhari ya yiwa Najeriya addu'a | Hoto: channelstv.com
Source: UGC

Haka kuma shugaban ya samu rakiyar mataimakansa da suka hada da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Garba Shehu da shugaban kula da harkokin kasa Lawal Kazaure.

Hakazalika, likitan shugaban kasa, Suhayb Rafindadi da babban jami'in tsaro, Idris Ahmed duk suna tare da shugaban.

Shugaban da ‘yan tawagarsa sun samu nasarar kammala ibadar a dakin Ka’aba a ranar Alhamis da misalin karfe 3:20 na safe agogon kasar.

Shugaba Buhari ya kai ziyara kasar Saudiyya ne karo na biyar don halartar wani taron zuba hannun jari da aka gudanar a birnin Riyadh na kasar Saudiyya.

Shugaban ya dan yi tattaki a birnin Madina domin gudanar da addu'o'in Allah ya dawo da zaman lafiya a Najeriya da farfadowar tattalin arzikin da cutar Korona ta shafa.

Read also

Bidiyoyin Buhari a Masallacin Annabi, ya kwarara wa Najeriya addu'o'in zaman lafiya

Shugaban da tawagarsa sun gudanar da irin wannan addu’a a Masallacin Harami da ke Makkah, yayin da suke gudanar da aikin Umrah, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Shugaba Buhari ya isa Saudiyya gabannin taron zuba jari

A baya mun kawo rahoton cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa birnin Riyadh, kasar Saudiyya gabannin taron zuba jari a daren ranar Litinin, 25 ga watan Oktoba.

Bayan isarsu filin jirgin sama na Sarki Khalid, Shugaban kasar da tawagarsa sun samu tarba daga mataimakin gwamnan Riyadh, Yarima Mohammed bin Abdulrahman Abdulaziz.

Shugaba Buhari tare da sauran shugabannin duniya, za su halarci bude taron a ranar Talata, 26 ga watan Oktoba.

Source: Legit

Online view pixel