Labarin Hotuna: Dangote, AbdulSamad, Mangal, Shugaba Buhari sun gudanar da aikin Umrah

Labarin Hotuna: Dangote, AbdulSamad, Mangal, Shugaba Buhari sun gudanar da aikin Umrah

Saudi Arabia: Manyan attajirai da yan kasuwa sun garzaya Makkah domin gudanar da aikin Umrah bayan taron zuba jarin da suka halarta tare da shugaba Muhammadu Buhari a Riyadh.

Hakazalika Shugaba Buhari tare da hadimansa sun shiga Ibadar da yammacin Laraba, 27 ga watan Oktoba, 2021.

Daga cikin attajiran akwai Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote; Shugaban kamfanin BUA, Alhaji Abdul Samad Rabiu; da Shugaban kamfanin MaxAir/AFDIN, Alhaji Dahiru Mangal.

An ga hotunan manyan attajiran tare.

Hakazalika hotunan shugaba Muhammadu Buhari tare da Ministan sadarwa, Dakta Isa Ibrahim Pantami, lokacin da aka karbi bakuncinsu.

Kalli hotunan:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Labarin Hotuna: Dangote, Abdus Samad Rabiu sun gudanar da aikin Umrah tare da Buhari
Labarin Hotuna: Dangote, Abdus Samad Rabiu sun gudanar da aikin Umrah tare da Buhari
Source: Facebook

Read also

Bidiyoyin Buhari a Masallacin Annabi, ya kwarara wa Najeriya addu'o'in zaman lafiya

Labarin Hotuna: Dangote, Abdus Samad Rabiu sun gudanar da aikin Umrah tare da Buhari
Labarin Hotuna: Dangote, Abdus Samad Rabiu sun gudanar da aikin Umrah tare da Buhari Hoto: Garba Shehu

Buhari a Masallacin Annabi, ya kwarara wa Najeriya addu'o'in zaman lafiya

A ranar Laraba, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karasa Birnin Makkah da ke kasar Saudiya domin yin Umrah.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, a wata takarda da ya fitar, ya ce Buhari da tawagarsa sun yi wa Najeriya da jama'ar ta fatan samun zaman lafiya da tsaro.

Kamar yadda Shehu ya bayyana, ya ce addu'o'in har da na fatan habakar tattalin arziki bayan annobar korona domin karuwar kasar nan da jama'ar ta.

Sun kwashe tsawon lokaci a cikin Masjid Annabawi inda suka dinga addu'o'i da karatun Al-Qur'ani mai girma.

Source: Legit.ng

Online view pixel