Ahmad Yusuf
11536 articles published since 01 Mar 2021
11536 articles published since 01 Mar 2021
Shugaban PDP na ƙasa, Ambasada Umar Damagum ya kara samun goyon baya yayin da ake shirin taron majalisar zartaswa NEC a makon gobe, 28 ga Nuwamba.
Gwamna Monday Okpebholo na Edo ya sallami dukkan ƴan majalisar gudanarwa na manyan makarantun gaba da sakandire mallakin gwamnatin jihar Edo nan take.
Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da kashe mutum guda yayin da faɗa ya kaure tsakanin wasu jami'anta da ke bakin aiki da wani sojan Najeriya a jihar Ebonyi.
Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci sojojin Najeriya su yi haɗin guiwa da mazuana yankuna a Kebbi domin kafa wani tsari da dabarar daƙile ayyukan Lakurawa.
Rahotanni sun bayyana cewa mutane sun ɓalle da zanga-zanga kan zargin da ake yaɗawa cewa ƴan sanda sun harbi shugaban hukumar kula da sufuri ta jihar Osun.
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya amince da N75,000 a matsayin sabon albashi mafi kankanta da gwamnatinsa za ta fara biyan ma'aikata nan ba da daɗewa ba.
Jam'iyyar PDP ta sha kashi a hannun APC a zaben gwamnan jihar Ondo da aka kammala ranar Asabar, wannan ne rashin nasara mafi muni da ta yi tun 1999.
Gwamna Monday Okpebholo ya samu damar naɗa hadimai 20 bayan majalisar dokokin jihar Edo ta amince da bukatarsa a zaman yau Talata, 19 ga watan Nuwamba.
Rundunar sojin Birged ta 6 ta samu nasarar tarwatsa mafakar ƴan bindiga a wasu kanann hukumomin jihar Taraba domin ba manoma damar girbin amfanin gona.
Ahmad Yusuf
Samu kari