Ahmad Yusuf
11508 articles published since 01 Mar 2021
11508 articles published since 01 Mar 2021
Hukumar kididdiga ta ƙasa watau NBS ta bayyana cewa an samu ƙarin hauhawar farashin kayayyaki daga 23.18% a watan Fabrairu zuwa 24.23% a watan Maris, 2025.
Rahotanni sun bayyana cewa tsohon shugaban riƙo na karamar hukumar Talata Mafara da tsohon kansila na cikin waɗanda aka kashe a harin garin Morai a Zamfara.
Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran NNPP na ƙasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya yi Allah wadai da harin da ƴan bindiga suka kashe gomman mutane a Filato.
Wasu miyagun ƴan bindiga sun farmaki wurin ibada a lokacin da mutane ke tsakiyar bautar Ubangiji a tsaunin Lokoja, sun sace mutane da dama da daddare.
Jigon PDP kuma mamba a kwamitin amintattu (BoT), Bode George ya bayyana cewa ba zai yiwu a sake ba Atiku Abubakar takara ba a 2027 saboda ya saɓa doka.
Wata kungiya mai rajin kare hakkin ɗan adam watau RID ta bukaci gwamnatin jihar Kano ta sauya dokokin ɓatanci sakamakon hukuncin da kotun koli ta yanke.
Babbar kotun jihar Oyo ta yi fatali da karar da wasu mutum 4 ƴan gidan sarauta suka shigar, suna kalubalantar naɗin sarkin Orile Igbon (Olugbon na Orile Igbon).
Yayin da PDP ke kokarin ɗinke barakarta, shugaban ƙaramar hukumar birni a Abuja watau AMAC, Hon. Christopher Zakka Maikalangu ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.
Shugaban Izala ta Najeriya, Dr. Abdullahi Bala Lau ya yi ta'aziyyar rasuwar shugaban Ahlus Sunnah na ƙasar Togo, Sheikh Abdul-Jalilu Nyandu, ya masa addu'a.
Ahmad Yusuf
Samu kari