Dalilan da Suka Jawo Buhari Ya Fatattaki Shugaban NYSC Daga Yin Wata 6 a Ofis
- Birgediya Janar Muhammad Fadah bai dade a kan kujerar NYSC ba, shugaban kasa ya sallame shi
- Bayan Manjo Janar Ibrahim Shuaibu ya bar hukumar ne sai aka nada Brig Gen MK Fadah a watan Mayu
- Ana jifan NYSC DG da badakalar satifiket, shekaru, rashin sanin aiki, da nuna son kai wajen aikinsa
Abuja - Bayanai sun fito game da abin da ya sa Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke Muhammad Fadah daga kujerar shugaban hukumar NYSC.
Birgediya Janar Muhammad Fadah bai wuce watanni shida yana rike da hukumar kula da harkar bautan kasa ba, Shugaban Najeriya ya yi waje da shi.
Bayanan da Premium Times ta samu ya nuna cewa an zargi Janar Muhammad Fadah da laifuffukan nuna son kai da rashin gaskiya wajen aikinsa.
Haka ana tuhumar Sojan da nuna bambancin addini a yadda ya tafiyar NYSC.
An aika da korafi ga Minista
Shugabar majalisar da ke sa ido a kan aikin NYSC a Najeriya, Fatima Abubakar ta aika takarda zuwa ga Ministan wasanni da matasa a kan Darektan.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Tun farko majalisa tana zargin cewa akwai alamar tambaya a kan shaidar karatun Birgediya Janar Muhammad Fadah da shekarunsa a doron Duniya.
Fadah bai wanke kan shi ba
Kamar yadda wannan kebantaccen rahoto ya nuna, an bukaci Fadah ya wanke kan sa daga wannan zargi, amma ya gagara yin hakan, har aka sauke shi.
A wasikar da aka aikawa Sunday Dare, an ankarar da shi cewa sabon Darekta Janar din bai dauki aikinsa da gaske ba, kuma da alamun bai da kwarewa.
Sannan an jefi Janar Farah da rashin basira, wanda hakan bai dace ga wanda zai jagoranci ragamar matasan da za su zama manyan gobe a Najeriya ba.
Korafe-korafe akalla uku da ake da su a kan Darekta Janar din sun shiga hannun jama’a, don haka majalisar take ganin wannan zai iya bata mata suna.
Babu jituwa da Sunday Dare
A gefe guda, Ministan tarayya ya saurari korafin da aka gabatar, don haka ya rubutawa shugaban kasa takarda cewa ayi tunbuke shugaban na NYSC.
Rahoton yace duk da zargin da ake yi masa, an tuhumi Farah da rashin biyayya ga Minista da rashin bin doka, yana ganin tsawon kafansa ya kai shi ofis.
Babu kudin kula da jiragen sa
Kuna da labari Najeriya ta na amfani da jiragen saman Boeing Business Jet (Boeing 737-800/NAF 001), Gulfstream G550, da su Gulfstream V (Gulfstream 500.
Sai dai ana fuskantar matsaloli domin gwamnatin tarayya tana fama da karancin kudin kula da jiragen da saya masu kayan aikin da ake bukata wajen tashi.
Asali: Legit.ng