Gwamna El-Rufai ya gabatar da kasafin kudin 2022 ga majalisar dokokin Kaduna

Gwamna El-Rufai ya gabatar da kasafin kudin 2022 ga majalisar dokokin Kaduna

  • Gwamnatin jihar Kaduna ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2022 ga majalisar dokokin jihar
  • Gwamnan ya bayyana yadda gwamnati ta tsara kashe kudaden a bangarori daban-daban na rayuwa
  • Gwmanan ya kuma mika godiya ga majalisar dokokin bisa goyon bayan da suke bashi a mulkinsa

Kaduna - Gwamna Malam Nasiru El-Rufai ya gabatar da daftarin kasafin kudin shekarar 2022 na naira biliyan 233 ga majalisar dokokin jihar Kaduna a yau Talata 12 ga watan Oktoba.

Kasafin kudin yana dauke da bayanin kashe Naira biliyan 146 a fannin ayyuka da jari da kuma na Kashewa akai-akai da suka kai Naira biliyan 87.6 a shekarar.

Bayan da Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2022, El-Rufai ya gabatar kasafin kudin 2022
Gwamnan jihar Kaduna yayin gabatar da kasafin kudi | Hoto: The Governor of Kaduna State
Asali: Facebook

El-Rufa'i ya yi nuni da cewa rabe-raben da aka yi a cikin alkaluman kasafin kudin na shekarar 2022 sun yi nuni da kimar siyasa da ka'idojin shugabanci wanda a koda yaushe suke jagorantar kasafin kudi shida na baya da gwamnatinsa ta gabatar.

Kara karanta wannan

Kasafin kudi: Naira Biliyan 134 sun yi mana kadan inji ‘Yan Majalisar Najeriya

El Rufa'i ya ce alkaluman shekarar 2022 sun yi kasa da kasafin kudin 2021 na N237.52bn, wanda ke da N157.56bn na ayyuka da jari da kuma N79.96bn da aka tsara don kashewa akai-akai, kashi 66% zuwa 34% na jarin da ake samu.

A sanarwar da gwamnatin Kaduna ta fitar a shafinta na Facebook, gwamnan ya bayyana cewa abubuwan da aka sa a gaba na kasafin 2022 sun hada da Ilimi, Kiwon Lafiya da Kayayyakin more rayuwa, kamar dai na kasafin baya.

Gwamnan ya kuma mika godiyarsa ga majalisar dokokin jihar bisa goyon baya da suke ba gwamnatinsa da ta dukufa wajen ayyukan ci gaba da al'ummar jihar ta Kaduna.

Kalli cikakkiyar sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar:

Sauye-sauye 18 na mukamai da El-Rufai ya yi a ranar Litinin saboda wasu dalilai

Kara karanta wannan

Gwamna Matawalle ya rantsar da shugabannin gudunarwa a kananan hukumomi 14

A wani labarin, Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i ya yi garanbawul ga wasu mukaman jami'an gwamnatinsa ta jihar Kaduna.

Gwamnan ya bayyana sabbin sauye-sayuen ne a shafinsa na Facebook, inda ya ce, an yi sauye-sauyen don ciyar da bangarori daban-daban na gwamnatin gaba.

A cikin sanarwar da ta iso hannun Legit.ng Hausa, gwamnan ya ce, an yiwa kwamishinoni takwas daga cikin 14 sauyin ma'aikatu, inda wasu kuma sauyin bai shafi su ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel