Gwamna Matawalle ya rantsar da shugabannin gudunarwa a kananan hukumomi 14

Gwamna Matawalle ya rantsar da shugabannin gudunarwa a kananan hukumomi 14

  • Gwamnan jihar Zamfara ya nada shugabannin gudunawar a kananan hukumomi 14 na jihar
  • Gwamnan ya bukace su da su kasance masu riko da amana, su kuma yi aiki wajen dakile rashin tsaro
  • Hakazalika, ya gargadesu kan amfani da kudin gwamnati ba bisa ka'ida ba, ya kuma nemi a ba gwamnatinsa hadin kai

Zamfara - Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, Gwamnan jihar Zamfara Bello Mohammed Matawalle ya rantsar da shugabannin gudanarwa a kananan hukumomi 14 sannan ya umarce su da su bayar da fifiko kan zaman lafiya da tsaro.

Da yake gabatar da su a bikin a jiya Laraba, Matawalle ya gargadi sabbin shugabannin da aka nada da su tuna da kalubalen tsaro da jihar ke fuskanta.

Gwamna Matawalle ya rantsar da shugabannin gudunarwa a kananan hukumomi 14
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle | Hoto: vanguardngr.com
Source: Twitter

Ya kara da cewa:

Read also

An kashe manoma uku a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Filato

"Matsalar rashin tsaro ita ce babbar kalubale, don haka, ya kamata ku tashi tsaye ku yi aiki don tunkarar 'yan ta'adda a yankunan ku."

Ya kuma shawarce su da su kasance masu taka-tsantsan wajen sarrafa albarkatu, saboda gwamnati ba za ta lamunci ayyukan sakacin kudi ba. Gwamna Matawalle ya yi kira da a tallafawa gwamnati a yakin da ake yi da 'yan bindiga.

Ya kara da cewa:

"Mun kuduri aniyar shigar da jami'an tsaro da duk wasu hanyoyin da ake da su wajen yakar 'yan bindiga."

Ya ci gaba da cewa, gwamnatin jihar za ta yi iya bakin kokarinta don kawo karshen ta'addanci da tabbatar da dawowar zaman lafiya a jihar.

Zamfara na fama da mummunan matsalar rashin tsaro

Jihar Zamfara na daya cikin jihohin Arewa maso yammacin Najeriya da lamurran tsaro suka tabarbare, inda ake yawan samun hare-haren 'yan bindiga.

Read also

Gwamna ya yi kuka kan kashe-kashen da ake yi a jiharsa, ya roki Allah da Ya hukunta maharan

Rahotanni sun bayyana cewa, majalisar jihar ta Zamfara ta dakatar da wasu mambobinta bisa zargin hannu a ayyukan barna na 'yan bindiga a jihar.

Sai dai, a rahoton Premium Times, daya daga cikin 'yan majalisun ya yi watsi da jita-jitar da ake yadawa yana tare da 'yan bindiga masu addabar jihar.

Ku ba 'yan bindiga hadin kai don tsira da rayukanku, shawarin 'yan sanda ga 'yan Najeriya

Tribune Nigeria ta ruwaito cewa, a ranar Talatar da ta gabata ne Babbar Rundunar ‘Yan Sanda ta shawarci 'yan Najeriya da su ba da hadin kai ga masu garkuwa da mutane idan sun fada hannunsu don kare lafiyar su da kuma gujewa kashe su.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar (FPRO), Frank Mba, wani Kwamishinan 'yan sanda, ya ba da shawarar ne a Abuja yayin gabatar da mutane 48 da ake zargi da aikata manyan laifuka.

Read also

Ku ba 'yan bindiga hadin kai don tsira da rayukanku, shawarin 'yan sanda ga 'yan Najeriya

Wadanda ake zargin har da wani Haliru Mohammed mai shekaru 25 wanda ya shirya garkuwa da 'yar uwarsa, Binta, don ya karbi fansa saboda ya gaza biyanta bashin da ta ke binsa.

Source: Legit.ng

Online view pixel