Sauye-sauye 18 na mukamai da El-Rufai ya yi a ranar Litinin saboda wasu dalilai

Sauye-sauye 18 na mukamai da El-Rufai ya yi a ranar Litinin saboda wasu dalilai

  • Gwamnan jihar Kaduna ya sake fasalin wasu bangarori na kwamishinoni da sakatarorin dindindin na jihar
  • Wannan na zuwa ne daga hannun gwamnan, inda ya bayyana irin sauye-sauye da aka samu a ma'aikatu
  • Legit.g Hausa ta tattaro muku jerin sauye-sauyen da aka samu daga hannun Malam Nasir El-Rufai

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i ya yi garanbawul ga wasu mukaman jami'an gwamnatinsa ta jihar Kaduna.

Gwamnan ya bayyana sabbin sauye-sayuen ne a shafinsa na Facebook, inda ya ce, an yi sauye-sauyen don ciyar da bangarori daban-daban na gwamnatin gaba.

A cikin sanarwar da ta iso hannun Legit.ng Hausa, gwamnan ya ce, an yiwa kwamishinoni takwas daga cikin 14 sauyin ma'aikatu, inda wasu kuma sauyin bai shafi su ba.

Kara karanta wannan

Babu maganar wahalar man fetur, kungiyar NUPENG ta fasa tafiya yajin-aiki a yau

An lura cewa, takwas daga cikin kwamishinoni 14 sauyin bai shafe ba, inda ba a samu sauyi a ma'aikatun Kudi, Shari'a, Kiwon Lafiya, Gidaje da Ci gaban Birane, Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida da Ayyukan Jin Kai da Ci gaban Al'umma.

Da dumi-dumi: El-Rufai ya sake fasalin kwamishinoninsa, ya sabbin nade-nade
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Muhammad Sani Abdullahi, Shugaban Ma’aikata, ya koma Kwamitin Tsare-Tsare da Kasafin Kudi, matsayin da ya rike da kyau a wa’adin farko na Malam El-Rufai.

Wannan shi ne karo na biyu da ake mayar da wani babban ma’aikacin gwamnan zuwa matsayin Kwamishina. A shekarar 2019, Muhammad Bashir Saidu, wanda a lokacin shine Shugaban Ma’aikata, an sauya masa aiki zuwa Ma’aikatar Kudi.

Sabin sauye-sauye da gwamnan ya yi

  1. Ma'aikatar Muhalli: Jaafaru Sani
  2. Ma'aikatar Ayyukan Jama'a da Gine-gine: Thomas Gyang
  3. Ma'aikatar Ilimi: Halima Lawal
  4. Ma'aikatar Aikin Noma: Ibrahim Hussaini
  5. Ma'aikatar Karamar Hukumar: Shehu Usman Muhammad
  6. Ma'aikatar tsare-tsare da kasafin kudi: Muhammad Sani Abdullahi
  7. Ma'aikatar Kasuwanci, Kirkira da Fasaha: Kabir Mato
  8. Ma'aikatar Ci gaban Wasanni: Idris Nyam

Kara karanta wannan

‘Yan siyasan Arewa 10 da ke kan gaba wajen neman kujerar shugaban Jam’iyyar PDP

Jerin sabbin nade-naden

A bangare guda, gwamnan ya sake nade-nade don rike mukaman sarrafa yankunan Kaduna, Kafanchan da Zariya.

  1. Balaraba Aliyu-Inuwa jami'ar cikin garin Zariya
  2. Muhammad Hafiz Bayero jami'i a babban birnin Kaduna
  3. Phoebe Sukai Yayi jami'i a yankin Kafanchan

Hakazalika, sanarwar ta ce, El-Rufai ya amince da tura wadannan jami'ai ga ma'aikatu a jihar kamar haka:

  1. Umma Aboki Sakatariyar dindindin, Kwamitin Tsarawa da Kasafin Kudi
  2. Murtala Dabo, Shugaban zartarwa na Hukumar Daukar Nauyi
  3. Abubakar Hassan DG, Hukumar Kula da Lafiya ta Jihar Kaduna (KADCHMA)
  4. Tamar Nandul MD, Kamfanin Ci gaban Kasuwa da Gudanarwa na Kasuwar Kaduna
  5. Khalil Nur Khalil ES, Hukumar Inganta Zuba Jari ta Kaduna (KADIPA)
  6. Maimunatu Abubakar GM, Hukumar Kare Muhalli ta Kaduna (KEPA)

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

"Haka kuma gwamnatin ta sanar da nadin Farfesa Mohammed Sani a matsayin shugaban hukumar kula da ayyukan kananan hukumomi; Muhammed Muazu Muqaddas a matsayin Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) da Dokta Shuaibu Shehu Aliyu a matsayin Babban Sakatare.

Kara karanta wannan

Ya kamata 'yan Najeriya su fahimci ilimin Buhari don gane tasirinsa, Minista

"Gwamnan ya zabi Dr. Ishaya Sarki Habu (shugaba), Aminu Yusuf Musa, Engr. Rabiu Tanko da Rebecca Nnawo Barde a matsayin sabbin membobin Hukumar Sabis na Majalisar."

Bayan korar ministoci biyu, Buhari ya gargadi ministocinsa kan aikin tukuru

A bangare guda, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 11 ga watan Oktoba ya karanto dokar tarzoma ga ministoci a majalisar ministocinsa da sakatarorin dindindin a fadin ma'aikatu.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa shugaban ya bukaci jami'an da su dauki batutuwan aiwatar da ayyukan da aka dora masu da muhimmanci.

Shugaban ya ce yana da mahimmanci jami'an su sani cewa sauke nauyin ayyukansu da muhimmanci zai taimaka wa gwamnatin yanzu ta cimma burin ta da alkawuran da ta yiwa 'yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel