Da dumi-dumi: PDP na cikin matsala yayin da manyan 'yan majalisa 2 suka sauya sheka zuwa APC

Da dumi-dumi: PDP na cikin matsala yayin da manyan 'yan majalisa 2 suka sauya sheka zuwa APC

  • Jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Anambra ta rasa 'yan majalisarta guda biyu zuwa APC a ranar Laraba, 6 ga watan Oktoba
  • Onyebuchi Offor (Mazabar Ekwusigo) da Douglas Egbuna (Mazabar Onitsha ta Arewa) sun sanar da sauya shekarsu a zauren majalisar
  • A nashi martanin, kakakin majalisar ya taya sabbin 'yan majalisar na APC murna tare da yi musu fatan alheri

Awka, jihar Anambra - A ranar Laraba, 6 ga watan Oktoba, 'yan majalisa biyu a majalisar dokokin jihar Anambra sun sauya sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC).

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa 'yan majalisar, Onyebuchi Offor (Mazabar Ekwusigo), da Douglas Egbuna (Mazabar Onitsha ta Arewa), sun sanar da sauya shekarsu a zauren majalisar a Awka, ranar Laraba.

Read also

Katsina: ‘Yan sanda sun kama tsohuwar ma’aikaciyar hukumar NIS bisa damfara ta N47m

Da dumi-dumi: PDP na cikin matsala yayin da manyan 'yan majalisa 2 suka sauya sheka zuwa APC
PDP na cikin matsala yayin da manyan 'yan majalisa 2 suka sauya sheka zuwa APC Hoto: KOLA SULAIMON/AFP
Source: Getty Images

Offor wanda shi ne shugaban marasa rinjaye na majalisar ya ce ya tuntubi iyalinsa da mai ba shi shawara kan shawarar da ya yanke na barin PDP zuwa APC.

Ya yi bayanin cewa ya shiga APC ne domin mazabarsa ta dandana mulkin jam'iyyar a matakin tarayya, PM News ta kuma bayyanawa.

Egbuna shima ya bayyana cewa ya koma APC ne bayan tuntuba da dama.

Kakakin majalisar, Uche Okafor, ya taya ‘yan majalisar murna tare da yi musu fatan alheri a sabuwar jam’iyyarsu.

Sauya sheka: Gwamna Buni ya karbi mambobin majalisar jihar Anambra 11 zuwa APC

A gefe guda, mun kawo a baya cawa Gwamnan jihar Yobe, kuma shugaban kwamitin tsare-tsaren babban taron jam'iyyar APC na rikon kwarya, Mai Mala Buni ya karbi wasu jiga-jigan siyasar jihar Anambra daga wasu jam'iyyu zuwa APC.

Read also

An fara taron kwamitin zartarwa na jam'iyyar PDP a Abuja

Ana ci gaba da yawaita sauya sheka a cikin wannan shekara, lamarin da ya kawo cece-kuce a jam'iyyun siyasa daban-daban na Najeriya.

Legit.ng Hausa ta lura cewa, akalla 'yan majalisa daga jihar Anambra 11 suka sauya sheka zuwa APC wanda gwamnan ya karbe su cikin lumana.

Source: Legit Nigeria

Online view pixel