Katsina: ‘Yan sanda sun kama tsohuwar ma’aikaciyar hukumar NIS bisa damfara ta N47m
- Rundunar ‘yan sanda jihar Katsina sun kama Hajarat Egbunu wacce tsohuwar ma’aikaciyar hukumar kula da shige da fice ce
- Hakan ya biyo bayan yadda ta damfari wasu N47,000,000 da sunan za ta samar wa jama’a aiki a hedkwatar ECOWAS dake Abuja
- Har ila yau an kama wasu mutane 2 da ake zargin su na da hannu a damfarar a ranar Litinin, 4 ga watan Oktoban 2021
Jihar Katsina - Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wata Hajarat Egbunu wacce tsohuwar ma’aikaciyar hukumar kula da shige da fice, NIS ce bisa damfarar N47,000,000.
Bisa ruwayar The Cable, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, Gambo Isah ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Laraba, inda ya ce tuni aka kori Egbunu daga NIS.
A cewar Gambo, ana zargin matar mai shekaru 42 da amsar kudaden wasu masu neman aikin bisa alkawarin za ta nema mu su aiki a hedkwatar ECOWAS da ke Abuja.
An kama wasu da ake zargin ta hada kai da su wurin damfarar
An kama wasu mutane 2 da ake zargin su na da hannu a damfarar.
Kamar yadda The Punch ta ruwaito, Isah ya bayyana cewa:
“A ranar 4 ga watan Oktoban 2021 da misalin karfe 3:30 na rana bisa kokarin jami’an binciken sirri, rundunar ta kama wani Ibrahim Lawal El-Maki mai shekaru 45 na Rafin Dadi Quarters dake zaune yanzu a Gwarimpa Quarters a Abuja wanda ya hada kai da wata Hajarat Iyeh Egbunu mai shekaru 42 ‘yar jihar Kogi, wacce aka fatattaka daga hukumar kula da shige da fice kuma rikakkiyar ‘yar damfara ce da ake nema ido rufe bisa damfarar mutane da dama.”
“Lamarin da ya auku shine yadda wanda ake zargin, Ibrahim Lawal El-Maki a ranar 15 ga watan Afirilun 2020 ya samu Aminu Hamaza mai shekaru 32 a Katsina da batun nema ma sa aiki a hedkwatar ECOWAS da ke Abuja, inda zai dinga samun albashin fiye da N3,000,000.
“Ya sanar da shi cewa sai ya ajiye N3,500,000 kafin ya samu aikin. Aminu Hamza ya sanar da abokin sa wanda shi ma ya yi ra’ayin samun aikin. Daga nan su ka tattara N7,000,000 su ka tura asusun bankin El-Maki."
Daga bisani El-Maki ya tura ma sa takardar samun aiki ta WhatsApp wacce daga baya su ka gano ta bogi ce.
“Yayin bincike, an gano Ibrahim Lawal El-Maki kuma aka kama shi. Ya tabbatar da yadda ya amshi kudin ya bai wa Hajarat Iyeh Egbunu, da sunan za ta taimaka wa abokin sa ta sama ma sa aiki a ECOWAS.
“El-Maki ya taimaka wa ‘yan sanda wurin bincike wanda har su ka samu nasarar kama Hajarat Iye Egbunu, wacce ta tabbatar ta amshi N34,800,000 daga Ibrahim Lawal El-Maki ta banki.
“Saidai El-Maki ya bayyana cewa ta amshi N47,350,000 daga wurin shi.
“Sannan akwai mutane da dama wadanda Hajarat Iye Egbunu ta damfara ta wannan hanyar kuma su na ta tururuwar zuwa hedkwatar don kai korafin su.”
Gambo ya kara da cewa har yanzu su na ci gaba da bincike akan lamarin.
Hotunan mutumin da aka kama ya damfari mutane 64 miliyoyin naira a Kano
A wani rahoton daban, Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani hatsabibin dan damfara bisa zargin sa da amfani da sunan babban bankin Najeriya wurin yasar dukiyar mutane 64 ta hanyar amfani da takardun bogi, LIB ta ruwaito.
Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Laraba, 8 ga watan Satumba inda yace an kama wanda ake zargin, Buhari Hassan a Yankaba Quarters ne da ke jihar.
Asali: Legit.ng