An fara taron kwamitin zartarwa na jam'iyyar PDP a Abuja
- Shugabannin jam'iyyar Peoples Democratic Party sun hallara don taron kwamitin zartarwa na kasa karo na 94
- A yanzu haka ana gudanar da taron a hedikwatar jam'iyyar da ke Wadata Plaza, Wuse Zone 5, Abuja
- An umarci mambobin jam'iyyar da su kasance cikin taron don cimma matsaya kan matsayin shugaban jam'iyyar PDP
Babbar jam'iyyar adawa ta Najeriya, Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Alhamis, 7 ga watan Oktoba, ta fara taron gaggawa na kwamitin zartarwar jam'iyyar na kasa (NEC) karo na 94.
Taron wanda ke wakana a Abuja yana gudana ne a zauren NEC, hedikwatar PDP ta kasa, Wadata Plaza a Abuja.
A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren jam’iyyar na kasa, Umaru Tsauri, kuma Legit.ng ta gani, PDP ta umarci dukkan mambobinta da su shiga taron.
Hakanan, Punch ta rahoto cewa PDP NEC ita ce ta biyu mafi girma a bangaren yanke shawara na jam'iyyar adawa.
A taron, ana sa ran jam'iyyar da membobin NEC za su yanke hukunci na ƙarshe kan shawarwarin kwamitin shiyya da gwamna Ifeanyi Ugwuanyi ke jagoranta.
Tun da farko kwamitin ya ba da shawarar cewa shugaban PDP na kasa na gaba ya fito daga yankin arewa.
Sai dai kuma, game da amincewa da shawarwarin kwamitin, mambobin jam'iyyar sun yi gargadin cewa idan aka aiwatar da shi zai iya yin mummunan tasiri kan kudirin 'yan takarar shugaban kasa na arewa a PDP.
Shi ma da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, Shugaban Kwamitin Amintattu na PDP, Walid Jibrin, ya yi kira ga shugabannin jam'iyyar da su rika fifita maslahar al'umma gaba da ta su.
Atiku Abubakar ya yi magana kan yankin da ya kamata PDP ta kai takarar shugaban kasa
A gefe guda, Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, yace shugaban ƙasa na gaba zai iya fitowa daga kowane yanki, kamar yadda The cable ta ruwaito.
Atiku ya yi wannan magana ne ranar Alhamis a taron majalisar zaryarwa (NEC) na babbar jam'iyyar hamayya PDP, wanda ya gudana a Abuja.
Tsohon shugaban ƙasan yace yankin da shugaban ƙasa ya fito ba shine hanyar warware matsalolin da Najeriya ke fama da su ba.
Asali: Legit.ng