Sauya sheka: Gwamna Buni ya karbi mambobin majalisar jihar Anambra 11 zuwa APC

Sauya sheka: Gwamna Buni ya karbi mambobin majalisar jihar Anambra 11 zuwa APC

  • Gwamnan jihar Yobe ya karbi wasu jiga-jigan siyasar jihar Anmabra zuwa jam'iyyar APC
  • Wannan na fitowa ne daga cikin wata sanarwar da Daraktan yada labarai na gwamnan ya fitar
  • An samu halartar jiga-jigan APC da gwamnoni yayin da gwamna Buni ke karbar 'yan siyasar

Gwamnan jihar Yobe, kuma shugaban kwamitin tsare-tsaren babban taron jam'iyyar APC na rikon kwarya, Mai Mala Buni ya karbi wasu jiga-jigan siyasar jihar Anambra daga wasu jam'iyyu zuwa APC.

Ana ci gaba da yawaita sauya sheka a cikin wannan shekara, lamarin da ya kawo cece-kuce a jam'iyyun siyasa daban-daban na Najeriya.

Legit.ng Hausa ta lura cewa, akalla 'yan majalisa daga jihar Anambra 11 suka sauya sheka zuwa APC wanda gwamnan ya karbe su cikin lumana.

Bikin sauya sheka: Gwamna Buni ya karbi mambobin majalisar jihar Anambra 11 zuwa APC
Yayin da ake karbar jiga-jigan siyasar jihar Anambra | Hoto: Mamman Mohammed
Asali: Facebook

cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na gwamna Buni ya fitar a shafinsa na Facebook, mun samu cikakken bayani kan karbar wadannan sabbin shiga ga jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sheke ma'aikacin jinyan MSF da wasu mutum 2 a Zamfara

A cewar sanarwar:

"Gwamnan jihar Yobe kuma Shugaban Kwamitin Tsare-Tsaren Babban Taron APC na rikon kwarya ya karbi 'yan majalisa 11 da suka hada da 'yan majalisar wakilai biyar da hudu masu ci da kuma 'yan majalisar dokokin jihar Anambra guda biyu wadanda suka sauya sheka daga PDP da APGA zuwa APC."

Hakazalika, gwamnan ya taya su murnar shiga jam'iyyar, yana mai cewa sun yi shawari mai kyau da suka zabi jam'iyyar APC.

Sanarwar ta nakalto Buni yana cewa:

""Kun yanke shawarar da ta dace a lokacin da ya dace, za ku mori dukkan hakkoki da alfarmar jam'iyyar."

Za mu kawo mazabunmu ga APC

Da suke jawabin godiya da shiga jam'iyyar, jiga-jigan na jihar Anambra sun yi alkawarin yada jam'iyyar APC a yankunansu.

A cewar wani yankin sanarwar:

Kara karanta wannan

‘Yan IPOB sun kashe tsohon Sarki, Mijin tsohuwar Minista da Direban ‘Dan Majalisa a wata daya

"Sun yi alkawarin kawo mazabarsu ga jam'iyyar a zaben gwamnan Anambra da ke tafe."

Legit.n Hausa ta lura cewa, kakakin majalisar wakilai, Mista Femi Gbajabiamila, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Omo Agege, gwamnonin jihohin Imo, Kogi, Kano, Jigawa da Kebbi suna wajen yayin karbar 'yan siyasar.

Gwamnatin Buhari ta amince maza su ke tafiya hutu idan matansu sun haihu

A wani labarin, Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta amince da hakkin hutun kwanaki 14 na haihuwa ga ma’aikatan gwamnatin tarayya maza domin ba su damar sabawa da jariran da aka haifa musu.

Shugaban ma’aikatan tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan ce ta bayyana hakan ga manema labarai a fadar gwamnati a ranar Laraba, bayan taron FEC na makon nan wanda Yemi Osinbajo (SAN) ya jagoranta a fadar shugaban kasa da ke Abuja, The Nation ta ruwaito.

Ta ce an yi haka ne don ba da damar habaka kauna da kusanci tsakanin uba da jariri, ko haifaffe ko dan riko, musamman a farkon kwanakin rayuwar yaron.

Kara karanta wannan

Abun mamaki: Bidiyo da hotunan yadda Firayim ministan Ethiopia ya koma 'direban' Buhari

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel