Da dumi-dumi: Buhari ya nada Justis Hussein Baba-Yusuf a matsayin Babban Alkalin Birnin Tarayya

Da dumi-dumi: Buhari ya nada Justis Hussein Baba-Yusuf a matsayin Babban Alkalin Birnin Tarayya

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Justice Hussein Baba-Yusuf a matsayin babban alkalin babban birnin tarayya Abuja
  • Shugaba Buhari a cikin wata wasika a ranar Talata, 5 ga watan Oktoba, ya umurci majalisar dattijai da ta tabbatar da nadin Baba-Yusuf a mukamin
  • Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ne ya karanto wasikar shugaban kasar a zauren majalisar ranar Talata

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 5 ga watan Oktoba, ya nemi Majalisar Dattawa da ta tabbatar da Mai Shari’a Hussein Baba-Yusuf a matsayin Babban Alkalin Babban Birnin Tarayya (FCT).

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan ne ya karanto wasikar shugaban kasar a zauren majalisar a yayin zamansu na yau, jaridar The Nation ta ruwaito.

Da dumi-dumi: Buhari ya nada Justis Hussein Baba-Yusuf a matsayin Babban Alkalin Birnin Tarayya
Buhari ya nada Justis Hussein Baba-Yusuf a matsayin Babban Alkalin Birnin Tarayya Hoto: Femi Adesina
Source: Facebook

Buhari a ranar 14 ga watan Agusta ya nada Justice Baba-Yusuf a matsayin mukaddashin babban alkalin babban birnin tarayya.

Read also

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya yi ganawar sirri da Goodluck Jonathan

A watan Agusta, Babban Alkalin Najeriya, Mai Shari’a Ibrahim Tanko Muhammad, ya rantsar da Mai Shari’a Hussein Baba Yusuf a matsayin mukaddashin Babban Alkalin Kotun FCT, tare da sabbin alkalan Kotun daukaka kara ta kotun shari’a na FCT, Daily Nigerian ta ruwaito.

Musamman ya umarci Mai Shari'a Baba Yusuf da ya gudanar da harkokin shari'ar babban birnin tarayya FCT bisa doka, inda ya kara da cewa, "Duk wani abu sabanin haka ba zai sanya ku a tarihi mai kyau ba."

Ma'aikatar Shari'a ta sallami Alkalan kotun Shari'a biyu a jihar Borno

A wani labari na daban, mun kawo a baya cewa domin cigaba da tabbatar da wanzuwar adalci, hukumar jin dadin ma'aikatan sashen shari'a ta jihar Borno ta sallami Alkalan kotun shari'a biyu.

Read also

Da dumi-dumi: Allah ya yi wa Sanata Abdulazeez, kanin Mama Taraba, rasuwa

The Punch ta ruwaito cewa wannan na kunshe ne cikin jawabin da ma'aikatar ta saki ranar Talata, 7 ga Satumba, kuma Sakataren hukumar, S.K Jidda ya rattafa hannu, a Maiduguri.

Jidda yace an yanke wannan shawara ne a zaman da hukumar tayi.

Source: Legit.ng

Online view pixel