Ma'aikatar Shari'a ta sallami Alkalan kotun Shari'a biyu a jihar Borno
- An sallami Alkalan kotun Shari'a biyu kuma an dakatad da Alkalan Majsitare biyu a Borno
- Wani jami'in majalisar Alkalai yace an koresu ne bisa wasu laifuka da suka aikata
- Majalisar Alkalan na da hurumin hukunta Alkalai idan aka kamasu da laifi
Domin cigaba da tabbatar da wanzuwar adalci, hukumar jin dadin ma'aikatan sashen shari'a ta jihar Borno ta sallami Alkalan kotun shari'a biyu.
The Punch ta ruwaito cewa wannan na kunshe ne cikin jawabin da ma'aikatar ta saki ranar Talata, 7 ga Satumba, kuma Sakataren hukumar, S.K Jidda ya rattafa hannu, a Maiduguri.
Jidda yace an yanke wannan shawara ne a zaman da hukumar tayi.
Yace:
"Hukumar daga yanzu ta sallami Alkalin babbar kotu, Alkali Yakub. Wannan ya biyo bayan sakamakon binciken da akayi bayan kararsa da kungiyar cigabar Kwayam ta kai ofishin shugaban Alkalai."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Shugaban alkalan ya mika karar zuwa kwamitin amsa korarrafi inda aka gano cewa Alkalin ya bari an yi amfani da shi wajen cin zarafi."
"Hakazalika an koru Alkalin kotun Shari'a, Alkali El-Hassan, kan zama a kotun da ba huruminsa ba."
Kotu ta bada umurnin a duba lafiyar kwakwalwa da kunnen Sheikh Abduljabbar
A wani labarin muwa, kotun Shari'ar Musulunci dake shari'a kan kara da gwamnatin jihar Kano ta shigar da Sheik AbdulJabbar Kabara ya bada umurnin aje a duba lafiyar kwakwalwar Malamin.
Kotun dake zaune a Kofar Kudu ta bada wannan umurni ne a zaman da aka yi ranar Alhamis, 2 ga watan Satumba 2021, rahoton BBC.
A cewar kotun, akwai bukatar gwada kwakwalwa da kunnuwan Malam Abduljabbar a asibitin Dawanau da na Murtala saboda rashin maganar da yayi lokacin da aka karanto masa tuhume-tuhume 4 da ake masa.
Asali: Legit.ng