Da dumi-dumi: Allah ya yi wa Sanata Abdulazeez, dan uwan Mama Taraba, rasuwa
- Allah ya yi wa Sanata Abdulazeez, yayan tsohuwar ministar mata, marigayiya Hajiya Aisha Jummai, rasuwa
- Abdulazeez ya rasu ne a ranar Talata, 5 ga watan Oktoba, bayan gajeriyar rashin lafiya
- Marigayin ya wakilci yankin Taraba ta Tsakiya a tsakanin 1999 zuwa 2007
Tsohon sanata Abubakar Abdulazeez Ibrahim wanda ya kasance yayan marigayiya Hajiya Aisha Jummai Alhassan (Mama Taraba), ya rasu.
Marigayin mai shekaru 64 wanda ya rasu a gidansa da ke Jalingo a ranar Talata, 5 ga watan Oktoba, bayan gajeriyar rashin lafiya ya wakilci yankin Taraba ta Tsakiya a tsakanin 1999 zuwa 2007.
Bugu da kari, marigayi Ibrahim ya yi takarar kujerar gwamna a jihar sau biyu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.
Ya yi karatun Injiniya da Gudanar da Kasuwanci a Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya, jihar Kaduna, kuma shine mamallaki Makarantun Firamare da Sakandare na Ibramiyya da Kwalejin Ilimi ta Peacock a Jalingo.
Kamar yadda yake bisa koyarwar addinin Musulunci, za a yi jana’izar marigayin da karfe 1:30 na rana a fadar mai martaba sarkin Muri.
Sannan daga bisani za a binne shi a makabartar Jika da Fari, inda aka binne marigayiya ‘yar uwarsa, Sahara Reporters ta rahoto.
Idanu sun zubda hawaye, Jalingo ta cika tankam yayin da aka yi jana'izar Mama Taraba
A wani labarin kuma, mun kawo a baya yadda Jalingo, babban birnin jihar Taraba, ya cika tankam sakamakon jana'izar Hajiya AIsha Jummai Alhassan, tsohuwar ministan harkokin mata da walwalar yara, wacce aka fi sani da 'Mama Taraba'.
Gawarta ta isa filin sauka da tashin jiragen sama na Jalingo wurin karfe 5:15 na yamma kuma an kaita gidan mahaifinta dake kusa da gidanta a GRA Jalingo, Daily Trust ta ruwaito.
An kai gawar Jummai Alhassan fadar sarkin Muri wurin karfe 6:46 na dare kuma babban limamin Masallacin Jalingo, Imam Nuru Dinga ya ja dubban jama'a jana'izar.
Asali: Legit.ng