Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya yi ganawar sirri da Goodluck Jonathan
- Rahotanni da muke samu sun bayyana cewa, shugaba Buhari ya gana da tsohon shugaban kasa Jonathan
- An ce ba a san dalilin ganawar tasu kasancewar Jonathan bai magantu da manema labarai ba bayan ganawar
- Ana kyautata zaton sun gana ne kan batun tsaron Najeriya da kuma yiyuwar zawarcin Jonathan a APC
Abuja - Jaridar Daily Trust ta ce, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba 6 ga watan Oktoba ya yi wata ganawar sirri da tsohon shugaban kasa, Dakta Goodluck Jonathan, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Legit.ng ta tattaro cewa ba a san dalilin ziyarar ba saboda Jonathan bai yi magana da manema labarai ba bayan taron.
Sai dai kuma, an lura cewa tsohon shugaban, a matsayinsa na wakilin ECOWAS na musamman a Mali, yana ta yin taro akai-akai tare da Shugaba Buhari kan kasar ta Yammacin Afirka da ke fama da rikici.
Akwai kuma rade-radin cewa wasu jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulkin kasar suna zawarcin Jonathan da tikitin takarar shugaban kasa na 2023.
Buhari ya gana da shugaban NIS, ya bada sabon umarni kan iyakokin kasar nan
A wani labarin, Shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, NIS, Muhammed Babandede, a ranar Juma'a ya yi bayani ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan ayyukan NIS na kokarin tsare iyakokin kasar nan.
Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, a yayin jawabi ga manema labaran gidan gwamnati a karshen taron sirri da yayi da shuagaban kasa, Babandede ya ce NIS ta kirkiro da sabbin tsare-tsare domin duba yanayin shige da fice bakin haure a kasar nan ba bisa ka'ida ba.
Kamar yadda yace, hukumar ta samu kayan aiki masu kyau domin taimaka wa wurin fallasa jama'ar da ke zama a kasar nan ba bisa ka'ida ba bayan hatimin shigowa kasar nan nasu ya gama aiki.
Yanzu Yanzu: Na kai karar Malami gaban Buhari, kuma bai amince da dokar ta-baci ba a Anambra - Gwamna Obiano
Asali: Legit.ng