Tsadar kayan abinci: Buhari ya ɗora alhakin kan 'yan kasuwa, ya ce suna boye kaya don samun kazamar riba

Tsadar kayan abinci: Buhari ya ɗora alhakin kan 'yan kasuwa, ya ce suna boye kaya don samun kazamar riba

  • Duk da cewar adadin abincin da ake nomawa a Najeriya ya karu, farashin kayan abinci na ci gaba da hauhawa, wanda ke haifar da matsananciyar wahala a kasar
  • Shugaban kasa ya ce ’yan kasuwa ne ke haddasa hakan domin suna saye kayan abinci suna boyewa domin samun riba
  • Don magance hauhawar farashin kayan abinci, shugaban na Najeriya ya bukaci ma'aikatar noma ta hada kai da sauran hukumomi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ‘yan kasuwa za a zarga a kan hauhawar farashin kayan abinci a kasar.

A yayin jawabinsa na kasa baki daya don murnar cikar Najeriya shekaru 61 da samun ‘yancin kai a ranar Juma’a, 1 ga Oktoba, shugaban kasar ya ce ‘yan kasuwa sun haifar da karancin abinci ta hanyar boye kayayyaki don samun riba mai yawa.

Read also

'Yan fashi sun afka wa coci domin sace kudi, sun daba wa mai gadi wuka a Abuja

Tsadar kayan abinci: Buhari ya ɗora alhakin kan 'yan kasuwa, ya ce suna boye kaya don samun kazamar riba
Tsadar kayan abinci: Buhari ya ɗora alhakin kan 'yan kasuwa, ya ce suna boye kaya don samun kazamar riba Hoto: Femi Adesina
Source: Facebook

Shugaban na Najeriya ya bayyana cewa:

"Abin takaici ne, yayin da adadin abincin da ake nomawa a kasar ya ƙaru, farashin abinci yana ta hauhawa saboda boye wadannan kayan abinci da 'yan kasuwa ke yi don cin riba."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mafita

Don magance wannan matsalar, Shugaba Buhari ya umarci Ma’aikatar Noma da Raya Karkara da ta gyara Hukumar Kula da adana Abinci ta Kasa.

Ma'aikatar za ta kuma hada gwiwa da hukumomin tsaro, Hukumar Kula da Kayan Masarufi da kuma Majalisar Dokokin Tarayya don nemo mafita ta dindindin ga wadannan ayyukan na boye abinci da shugaban kasar ya bayyana a matsayin masu kawo cikas da rashin kishin kasa.

A cewar shugaban na Najeriya, bangaren aikin gona ya kasance mabuɗin ci gaban tattalin arzikin ƙasar.

Ya kara da cewa don ci gaba da inganta noman abinci, an kammala sabbin madatsun ruwa da dama yayin da wasu hukumomin raya Kogi, musamman domin taimaka wa harkar noman rani.

Read also

Shekarau ya ba Gwamnonin jihohin Kudu shawara, yace su daina barazana kan batun 2023

Zanga-zangar Buhari-must-go na gudana a Abuja a ranar bikin samun 'yancin kai na 61

A wani labarin kuma, masu zanga-zangar da sanyin safiyar Juma’a, 1 ga watan Oktoba, sun mamaye gadar Dantata da ke kan shaharariyar hanyar filin jirgin sama a Abuja, suna neman shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi murabus.

Zanga-zangar ta zo daidai da bikin cikar kasar shekaru 61 da samun ‘yancin kai.

Masu zanga-zangar, dauke da manyan tutoci, sun cinna wuta a kan babbar hanyar.

Source: Legit

Online view pixel