Zanga-zangar Buhari-must-go na gudana a Abuja a ranar bikin samun 'yancin kai na 61

Zanga-zangar Buhari-must-go na gudana a Abuja a ranar bikin samun 'yancin kai na 61

  • A yanzu haka, ana nan ana gudanar da zanga-zangar Buhari-must-go a babbar birnin tarayya, Abuja
  • Masu zanga-zangar sun mamaye gadar Dantata da ke kan shaharariyar hanyar filin jirgin sama a Abuja, suna neman shugaban kasa Buhari ya yi murabus
  • Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake bikin samun yancin kan kasar karo na 61 a yau Juma'a, 1 ga watan Oktoba

Masu zanga-zangar da sanyin safiyar Juma’a, 1 ga watan Oktoba, sun mamaye gadar Dantata da ke kan shaharariyar hanyar filin jirgin sama a Abuja, suna neman shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi murabus.

Zanga-zangar ta zo daidai da bikin cikar kasar shekaru 61 da samun ‘yancin kai.

Zanga-zangar Buhari-must-go na gudana a Abuja a ranar bikin samun 'yancin kai na 61
Zanga-zangar Buhari-must-go na gudana a Abuja a ranar bikin samun 'yancin kai na 61 Hoto: ABN TV
Asali: UGC

Masu zanga -zangar, dauke da manyan tutoci, sun cinna wuta a kan babbar hanyar.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa 'yan sanda dauke da makamai sun tarwatsa masu zanga -zangar.

Kara karanta wannan

Labarin gimbiyar da ta bar masarautarsu ta auri talaka ya dauki hankalin jama'a

An tattaro cewa masu zanga -zangar dai sun hallara a wurin taron don fara aiwatar da zanga-zangar lokacin da jami'an 'yan sandan Najeriya suka mamaye yankin.

Sun harba hayaki mai sa hawaye sannan suka fatattake su.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito cewa mai fafutukar kare hakkin dan adam, Omoyele Sowore a ranar Alhamis ‘yan Najeriya su yi zanga -zanga a duk fadin kasar a ranar samun‘ yancin kai don yin watsi da Shugaba Muhammadu Buhari.

Sai dai kuma, ba za a iya tabbatar da ko an kama kowa ba har zuwa lokacin kawo wannan rahoton.

Bikin yancin kai: ‘Yan Najeriya sun yi martani yayin da Shugaba Buhari ya yi kira ga hadin kai

A wani labarin, mun ji cewa biyo bayan kiran da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi na hadin kan kasar, yan Najeriya da dama sun shiga shafukan sada zumunta don maida martani akan kalamansa.

Kara karanta wannan

An yi jana'izar mahaifin kakakin majalisar Zamfara da ya rasu a hannun 'yan bindiga

Yayin da mutane da yawa suka zarge shi kan yanayin da haɗin kan ƙasar ke ciki a halin yanzu wanda yake a mafi ƙanƙantarsa, wasu kuma sun yaba masa da yin aiki mai kyau don haɗa kan ƙasa.

Ku tuna cewa wasu mutanen kudu maso gabas da kudu maso yamma suna ta kira ga neman ballewa kan abin da suka bayyana a matsayin rashin adalci daga arewa da kuma mummunan yanayin tattalin arzikin da ke fuskantar al’umma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel