An yi jana'izar mahaifin kakakin majalisar Zamfara da ya rasu a hannun 'yan bindiga

An yi jana'izar mahaifin kakakin majalisar Zamfara da ya rasu a hannun 'yan bindiga

  • A yau Litinin aka yi jana'izar mahaifin kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara da ya mutu
  • An ba da sanarwar cewa, mahaifin nasa ya rasu sanadiyyar mutuwar zuciya a maboyar 'yan bindiga
  • An yi sallar jana'izar tasa ne duk da cewa ba a gano inda gawarsa take ba, wanda hakan karbabben abu ne a Muslunci

Zamfara - An yi sallar jana'izar Muazu Magarya, mahaifin kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara, Nasiru Magarya, Punch ta ruwaito.

An yi sallar jana'izar, wadda Sheikh Ahmed Umar Kanoma ya jagoranta ranar Litinin, 4 ga watan Oktoba a gidan kakakin majalisar da ke Gada-biyu Gusau, duk da cewa ba a gano gawar mamacin ba.

Da yake yiwa manema labarai karin haske jim kadan bayan sallar jana’izar, Kwamishinan Harkokin Addini, Sheikh Tukur Sani Jangebe, ya bayyana cewa za a iya yin sallar jana’izar musulmi da ya mutu yayin da gawarsa ke wani wuri.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Sanata na goyon bayan IPOB, ya ce akwai kungiyoyin aware a kudu sun fi 30

An yi jana'izar mahaifin kakakin majalisar Zamfara da ya mutu a hannun 'yan bindiga
Kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya ce:

"Ana yin sallar jana'izar da ake kira 'Salatul gha'ib' ga Musulmin da ya mutu kuma ba a ga gawarsa ba".

Maharan kakakin majalisar da wasu 'yan uwansa biyar 'yan bindiga sun sace su makonni takwas da suka gabata.

Sai dai ‘yan bindigar sun saki mambobi biyar da aka yi garkuwa da su kuma sun sanar da cewa mahaifin kakakin majalisar ya mutu ne sakamakon bugun zuciya a maboyarsu.

Mutane sun yi tururuwa zuwa gidan kakakin majalisar domin yi masa ta'aziyyar rasuwar mahaifinsa.

Mahaifin kakakin majalisa da malamin jami'a sun mutu a hannun 'yan bindiga

Alhaji Muazu Abubakar, mahaifin kakakin majalisar jihar Zamfara, Nasiru Muazu Magarya, ya rasu sakamakon bugun zuciya yayin da yake tsare a mafakar 'yan bindiga.

Babban dan uwan marigayin, Malam Dahiru Saraki Magarya ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a ranar Asabar, kamar yadda jaridar Blueprint ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Allah ya yi wa Sanata Abdulazeez, kanin Mama Taraba, rasuwa

An yi garkuwa da marigayin ne makonni takwas da suka gabata tare da matarsa, jariri dan makonni uku, Malam Magarya da wasu mutum biyu.

'Yan sanda sun cafke tsageru 13 da ake zargi 'yan bindiga ne kuma barayin shanu a Katsina

A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda a jihar atsina ta cafke mutane 13 da ake zargi da hannu a fashi da makami, satar shanu, garkuwa da mutane da safarar makamai da kuma ta’addancin kan 'yan jihar da ba su ji ba su gani ba.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a jihar Katsina, Gambo Isah ne ya bayyana hakan, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mista Isah ya ce kamun wadanda ake zargin ya kasance wani bangare na nasarorin da rundunar 'yan sandan jihar ta samu a baya-bayan nan a ci gaba da yaki da miyagun laifuka da aikata laifuka a jihar.

Kara karanta wannan

Ba na cikin matsananciyar bukatar takarar shugabancin kasa, Gwamnan Bauchi

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.