Da dumi-duminsa: Shugaba Buhari ya yi sabon nadi mai muhimmanci

Da dumi-duminsa: Shugaba Buhari ya yi sabon nadi mai muhimmanci

  • Don ci gaba da aiwatar da ajandarsa ta Next Level, Shugaba Buhari ya nada sabon MD na FMC, Bida
  • Sabon nadin shine Dakta Usman Abubakar, wanda ya karbi ragamar aiki daga hannun Muhammad Usman-Aminu a ranar Talata, 14 ga watan Satumba
  • Karamin ministan lafiya, Olorunnimbe Mamora ne ya sanya hannu kan wasikar nadin Usman

Bida, Jihar Neja - A ranar Alhamis, 30 ga watan Satumba, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Dr Usman Abubakar a matsayin sabon daraktan kiwon lafiya na cibiyar lafiya ta tarayya (FMC) Bida, jihar Neja.

Nadin Abubakar na kunshe ne a cikin wata wasika da Olorunnimbe Mamora, karamin ministan lafiya ya sanya wa hannu a ranar Alhamis.

Da dumi-duminsa: Shugaba Buhari ya yi sabon nadi mai muhimmanci
Shugaba Buhari ya nada sabon MD na FMC, Bida Hoto: Femi Adesina
Source: Facebook

Nadin, wanda ya zo bayan karewar wa’adin tsohon shugaban na FMC, Dr Muhammad Usman-Aminu, zai fara aiki daga ranar Talata, 14 ga watan Satumba, jaridar The Nation ta ruwaito.

Read also

Yanzu-Yanzu: Bayan kimanin wata ɗaya ana fafatawa, likitocin Najeriya sun janye yajin aiki

Da yake taya sabon daraktan murna, Shugaba Buhari ya bayyana a cikin wasikar cewa sabon matsayin zai taimaka wajen tallafa wa ajandarsa ta Next Level.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani bangare na wasikar ya ce:

"Ana sa ran za ka yi aiki tuƙuru don tabbatar da ganin cewa asibitin ya ci gaba da ba da ingantaccen kiwon lafiya sannan ka yi ƙoƙarin inganta nasarorin da kuma barin alamar nasararka a cibiyar.
"Ina kuma roƙonka da ka tabbatar da yardar da aka ba ka ta wannan nadin sannan kuma kayi aiki tare da duk masu ruwa da tsaki don samar da zaman lafiya na masana'anta don tallafawa ajandar Shugaban kasa na Next Level."

PM News ta ruwaito cewa a cikin martaninsa, Abubakar ya ce:

"Na yi alƙawarin kiyaye ƙa'idodin aikin Likitanci da na ma'aikatan gwamnati."

Read also

Jagororin PDP sun fara yaki domin David Mark ko Makarfi ya karbi shugabancin Jam’iyya

A wani labari na daban, Gwamna Babagana Umara Zulun ba jihar Borno a ranar Laraba ya zargi daukan jami'an tsaro da hukumomin tsaron Najeriya ke yi aiki da saka siyasa a lamarin, abinda ke saka fannin tsaron kasar nan cikin mawuyacin hali.

Zulum na yin jawabi ne mai take 'Ungoverned Space and Insecurity in the Sahelian Region: Implications for Nigeria Domestic Peace and Security' a NIPSS da ke Kuru, jihar Filato, Daily Trust ta wallafa.

Source: Legit.ng

Online view pixel