Yanzu-Yanzu: Bayan kimanin wata ɗaya ana fafatawa, likitocin Najeriya sun janye yajin aiki

Yanzu-Yanzu: Bayan kimanin wata ɗaya ana fafatawa, likitocin Najeriya sun janye yajin aiki

  • Kungiyar likitocin Nigeria ta janye yajin aikin da ta shafe kimanin wata daya tana yi
  • Kungiyar ta sanar da janye yajin aikin ne bayan taron da ta yi daga ranar Lahadi zuwa Litinin
  • Kungiyar ta ce ta yi nazarin nasarorin da aka samu kawo yanzu hakan yasa ta umurci mambobinta su koma aiki ranar Laraba

Abuja - Kungiyar likitocin Nigeria masu neman kwarewa, NARD, ta janye yajin aikin da ta shafe kimanin wata daya tana yi, likitocin za su koma bakin aiki a ranar Laraba, Vangaurd ta ruwaito.

Idan za a iya tunawa, a watan Agusta ne kungiyar likitocin ta shiga yajin aikin bayan rashin jituwa tsakanin ta da gwamnatin tarayya kan rashin kayan aiki a manyan asibitocin kasar.

Read also

Dalilin da yasa muka janye yajin aiki bayan shafe watanni biyu muna fafatawa, Likitoci

Yanzu-Yanzu: Bayan kimanin wata ɗaya an fafatawa, likitocin Najeriya sun janye yajin aiki
Likitocin Nigeria. Hoto: Vanguard Ngr
Source: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin wani sakon bayan taro mai dauke da sa hannun sakataren kungiyar likitocin Nigeria, Ekpe Philips Uche, bayan taron da wakilan NMA da NARD suka yi a ranar Lahadi a Abuja, NMA ta shawarci NARD ta da janye yajin aikin.

A wurin taron, NMA ta bukaci shugabannin kwamitin ofisoshi, NOC, ta tabbatar ta aiwatar da abubuwan da suke cikin yarjejeniyar da ta yi da gwamnatin tarayya a ranar 21 ga watan Agusta.

Kungiyar ta bukaci NOC ta rika sanar da majalisar kolin NMA nasarorin da ake samu game da aiwatar da abubuwan da ke cikin yarjejeniyar.

NMA ta kuma bukaci NOC ta cigaba da tuntubar shugabannin jihohi har ma da na Abuja kan nasarorin da ake samu wurin aiwatar da abubuwan da ke cikin yarjejeniyar.

Read also

Hadimin Jonathan ya bayyana kudirin neman takarar Shugaban kasa, ya shimfida alkawura

A cewar shugaban NARD na kasa, Godiya Ishaya, kungiyar ta janye yajin aikinta a hukumance.

Ya ce:

"Mun janye yajin aikin mu, za mu koma bakin aiki karfe 8 na safen ranar Laraba. A safiyar yau muka cimma wannan matsayar.
Mun yi taron gaggawa daga karfe 5.30 na yamma zuwa safiyar yau kuma NEC ta yanke shawarar a janye yajin aikin duba da nasarorin da aka samu kawo yanzu."

Yajin aikin likitocin ya shiga sati na tara kenan a ranar Litinin, hakan ya durkusar da ayyuka a asibitocin gwamnati da ke kasa, lamarin da ya jefa marasa lafiya cikin wahala.

Mutane su na barazanar halaka ni, Likitan Najeriya da ya buɗe wurin gwajin DNA tare da yin rahusa na kashi 70

A wani labarin daban, wani likita wanda ya bude wurin gwajin kwayoyin halitta na DNA a anguwarsu ya bayyana yadda wasu mutane suke barazanar halaka shi a shafin sa na dandalin sada zumunta sakamakon zargin zai zama kalubale ga aurensu.

Read also

Bishiya mai shekaru 100 ta fadi kan mutane, ta hallaka jariri da mahaifiyarsa

Kamar yadda Pulse Nigeria ta ruwaito, likitan mai suna Dr Penking ya bayyana cewa zai bude wurin gwajin DNA din a jihar Legas ne kuma zai samar da rahusar kaso 75 bisa dari a watan Oktoba.

Mutane da dama sun yarda da cewa wannan rahusar za ta bai wa maza da yawa damar tabbatar wa idan su ne iyayen yaran su na hakika, hakan ya kada ruwan cikin jama’a.

Source: Legit

Online view pixel