Jagororin PDP sun fara yaki domin David Mark ko Makarfi ya karbi shugabancin Jam’iyya

Jagororin PDP sun fara yaki domin David Mark ko Makarfi ya karbi shugabancin Jam’iyya

  • A halin yanzu PDP ta na neman wanda zai zama sabon shugaban jam’iyya na kasa
  • Ana rade-radin Gwamnonin jam’iyyar suna so David Mark ya gaji Uche Secondus
  • Wasu kuma suna goyon bayan Ahmad Makarfi ya zama shugaban jam’iyyar PDP

Abuja - Wasu kusoshi a jam’iyyar PDP sun fara kokarin ganin Sanata David Mark da Sanata Ahmed Muhammad Makarfi sun zama shugaban jam’iyya.

Kwamitin Ifeanyi Ugwuanyi ya canza lissafin da ake yi a PDP bayan ya bada shawarar sabon shugaban jam’iyya ya fito daga yankin Arewacin Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa daga cikin wadanda ake kokarin ganin sun karbi ragamar PDP akwai Ahmed Muhammad Makarfi da David Mark.

Takarar David Mark

Rahoton yace gwamnonin PDP ne suke kokarin tallata takarar Mark. Baya ga haka, gwamnan jiharsa watau Samuel Ortom yana cikin masu mara masa baya.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC za ta yaki satar kudin fanshon ma’aikata, wasu mutane sun wawuri N150bn

Gwamnonin jam’iyyar adawar suna ganin Sanata Mark zai iya kwantar da rikicin da ke cikin PDP.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiya tace jam’iyyar PDP tana neman wanda zai samu karbuwa a ko ina, wanda zai samu goyon bayan sojoji da 'yan siyasa, kuma bai taba sauya-sheka ba.

Jagororin PDP
David Mark, Jonathan da manyan PDP Hoto: thewhistler.ng
Asali: UGC

“A 2015 bayan PDP ta rasa zabe, kusan kowa da ake ji da shi a jam’iyya, ya bi APC. Shi kuma ya yi zamansa a haka, wannan abu da ya yi ne yake yi masa rana.”

Ahmad Makarfi zai sake rike PDP?

Haka zalika ana rade-radin cewa wasu a gefe guda suna so tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmad Makarfi ya zama sabon shugaban jam’iyyar PDP na kasa.

Da aka tuntubi Sanata Makarfi a kan wannan batun, sai ya nuna cewa shi bai da wannan labari.

Kafin Prince Uche Secondus ya zama shugaban PDP, Makarfi ya rike kujerar na rikon kwarya. Tsohon Gwamnan yana cikin wadanda ba su taba barin PDP ba.

Kara karanta wannan

Hadimin Jonathan ya bayyana kudirin neman takarar Shugaban kasa, ya shimfida alkawura

Chukwunweike Maduekwe ya doke PDP a kotu

A makon da ya wuce ne ku ka samu rahoto cewa bayan shekaru fiye da shida da yin zaben 2015, wani ‘Dan takarar ‘Dan Majalisa ya samu galaba a kan PDP a kotu.

Alkali yace Jam’iyyar PDP ta dawo wa Chukwunweike Maduekwe da Naira miliyan 4.5 da ya biya na sayen fam, wanda a karshe ba a shirya zaben fitar da gwani ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel