An siyasantar da diban ma'aikatan tsaro, Gwamna Zulum ya koka

An siyasantar da diban ma'aikatan tsaro, Gwamna Zulum ya koka

  • Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya zargi siyasantar da daukar aikin tsaro a kasar nan
  • A cewar gwamnan, gwamnoni, ministoci da wasu jiga-jigan gwamnati ne ke da guraben ayyukan
  • Ya kara da cewa, marasa aikin yi ake ba aikin ba wai masu son kawo karshen matsalar kasar nan ba

Filato - Gwamna Babagana Umara Zulun ba jihar Borno a ranar Laraba ya zargi daukan jami'an tsaro da hukumomin tsaron Najeriya ke yi aiki da saka siyasa a lamarin, abinda ke saka fannin tsaron kasar nan cikin mawuyacin hali.

Zulum na yin jawabi ne mai take 'Ungoverned Space and Insecurity in the Sahelian Region: Implications for Nigeria Domestic Peace and Security' a NIPSS da ke Kuru, jihar Filato, Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

Abun mamaki: Bidiyo da hotunan yadda Firayim ministan Ethiopia ya koma 'direban' Buhari

An siyasantar da diban ma'aikatan tsaro, Gwamna Zulum ya koka
An siyasantar da diban ma'aikatan tsaro, Gwamna Zulum ya koka. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kamar yadda Daily Trust ta wallafa, ya ce:

"Babbar matsala da ake samu wurin daukan aiki ne. Wadanda ake dauka aiki a rundunar sojin kasa, 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro duk masu neman aiki ne. Da yawa daga cikinsu sun je wurin ne saboda ba su da aikin yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wadanda aka dauka a shekaru 20 da suka gabata sun fi aiki mai kyau amma wadannan masu neman abun yin aiki kawai suke so a basu. Don haka babu mayar da kai tare da sadaukarwa a ayyukansu.
"A yanzu, gwamnoni, ministoci da sauran manyan jami'an gwamnati su ke da guraben aikin. Babu mai yi musu jarabawa ko sun dace da aikin ko akasin hakan. Daukar aikin soja, 'yan sanda da sauransu duk an siyasantar."

Gwamnan ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Ganduje, Amaechi, Ikweremadu, wasu mutum 22 da suke cin taliyar siyasa tun 1999 har yanzu

"Har sai mun yi a kan gyara komai, babu abinda zai sauya a kasar nan.
"Idan muna son cigaba, dole ne mu tantance abinda ya fi kyau. Idan ba haka ba, za mu cigaba da daukan sakarkaru aiki. Dole ne mu dauka wadanda za su iya abinda mu ke so saboda muna da masu kwazo da yawa a Najeriya."

El-Rufai: Sakarci ne ka kalmashe a Legas ko Fatakwal kana son a miko muku mulki

A wani labari na daban, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi karin haske kan matsayar kungiyar gwamnonin arewa kan mika mulki kudancin Najeriya, Daily Trust ta ruwaito hakan.

A wani taro a Kaduna a ranar Litinin, gwamnonin sun ce mulkin karba-karba na shugabancin kasa ba ya daga cikin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Sun sanar da hakan ne yayin martani ga bukatar takwarorinsu na kudu wanda suka bukaci yankinsu ya samar da shugaban kasa a nan gaba.

Kara karanta wannan

El-Rufai zai rusa dubunnan gidaje a Garin Zaria, Gwamnati za ta tada Unguwa sukutum

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel