Ya kamata 'yan Najeriya su yabawa Buhari bisa daina layin sayen man fetur, MURIC

Ya kamata 'yan Najeriya su yabawa Buhari bisa daina layin sayen man fetur, MURIC

  • Kungiyar MURIC ta bayyana yabo ga shugaba Buhari bisa daina layin man fetur a Najeriya
  • Ya bayyana haka ne yayin da ake kokarin dogon layin man fetur a kasar Burtaniya kwanan nan
  • MURIC ta ce, ya kamata 'yan Najeriya su zama masu yabo ga shugaba Buhari saboda yanzu sun daina layi

Kungiyar Kare Hakkokin Musulmai (MURIC) ta ce rikicin man fetur da ke gudana a Burtaniya wata dama ce ga 'yan Najeriya su yabawa Shugaba Muhammadu Buhari.

A cikin wata sanarwa, daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya ce a karkashin mulkin Buhari, Najeriya ta yi sallama da layin sayen man fetur.

Ya kamata 'yan Najeriya su yabawa Buhari bisa daina layin sayen man fetur, MURIC
Shugaban MURIC, Ishaq Akintola | Hoto: premiumtimesng.com
Source: UGC

A cewarsa:

“Burtaniya ta fada cikin karancin mai wanda ya haifar da dogayen layuka a gidajen mai a cikin makwanni biyu da suka gabata. Daga cikin gidajen mai 8,000 a Burttaniya, kusan kashi biyu bisa uku na gidajen mai 5,500 sun kare.

Read also

Yadda sojoji suka bankado yunkurin ISWAP na kai wa tubabbun Boko Haram farmaki

"An sanya sojojin Burtaniya cikin lamarin don shiga tsakani yayin da gwamnatin Boris Johnson ta ba da biza na wucin gadi ga direbobin tankar mai na kasashen waje 5,000. Burtaniya ta shiga matsala ta kuma jikkata.
“Lamarin ya haifar da rikicin zamantakewa da tattalin arziki a Burtaniya. An samu karancin abinci, cikowar tituna, musamman a gidajen mai. Layin mai yana wuce sa'o'i. Bugu da kari, gwamnati na duba yiwuwar rufe makarantu."

Da yake tuna dogayen layuka da suka ya tilastawa ‘yan Najeriya da yawa kwana a gidajen mai na tsawon kwanaki uku ko fiye, Akintola ya ce lamarin ya canza tun lokacin da Buhari ya hau mulki.

Ya kara da cewa:

“Wannan gaskiya ce tabbatacciya kuma ba za a iya musantawa ba. Dole 'yan Najeriya su jinjinawa Buhari. Ya zama dole mu yaba wa wannan gwamnatin musamman dangane da rashin dogon layi idan muna son mu kasance masu gaskiya.

Read also

DHQ ta karrama Laftanal Kanal Abu Ali, yariman da Boko Haram suka kashe a 2016

"Abubuwan da ke shaida hake shine Buhari ne shugaban da ya nemo maganin matsalar karancin man fetur da ta addabi Najeriya shekaru da dama kuma ya gagara samun mafita a karkashin shugabanin Najeriya uku.

Majalisar dattawa ta nemi Buhari ya fitar da N300bn don gyaran tituna a Neja

A wani labarin, Majalisar dattijai a ranar Talata ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta samar da Naira biliyan 300 a matsayin kudin taimakon gaggawa don gyara munanan hanyoyi a jihar Neja.

Wannan kuduri na babban zauren ya biyo bayan wani kudiri kan lalacewar hanyoyi a fadin jihar Neja da toshe hanyoyin ta hanyar nuna rashin amincewa da direbobin tirela da direbobin tanka suke yi a cikin kwanaki hudu da suka gabata.

Mataimakin Babban Bulaliyar Majalisar Dattawa, Sanata Aliyu Sabi Abudullahi, mai wakiltar Neja ta Arewa ne ya kawo kudirin, in ji rahoton The Nation.

Read also

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

Source: Legit Newspaper

Online view pixel