DHQ ta karrama Laftanal Kanal Abu Ali, yariman da Boko Haram suka kashe a 2016

DHQ ta karrama Laftanal Kanal Abu Ali, yariman da Boko Haram suka kashe a 2016

  • Yariman sojan da ya rasu a fagen fama, Laftanal Kanal Abu Ali, ya samu kambun girmamawa daga hedkwatar tsaro ta kasa
  • Jarumin sojan, wanda shi ne kwamandan bataliya ta 272 ya rasa ransa yayin da miyagun Boko Haram suka kai farmaki a 2016 a Borno
  • A lokacin rayuwar Ali, shi ne jarumin sojan da ya jagoranci rundunarsa wurin kwato Baga daga hannun 'yan Boko Haram a 2015

FCT, Abuja - Hedkwatar tsaro ta kasa (DHQ) ta karrama Muhammad Abu Ali, soja mai mukamin laftanal kanal kuma kwamandan bataliya ta 272 a baya wanda Boko Haram suka kashe a 2016.

TheCable ta ruwaito cewa, a ranar 4 ga watan Nuwamban 2016, 'yan ta'addan Boko Haram sun halaka Ali yayin da suka kai wa bataliya ta 119 farmaki da ke Malam Fatori a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari za ta fara biyan daliban digiri da NCE kudin kashewa

DHQ ta karrama Laftanal Kanal Abu Ali, yariman da Boko Haram suka kashe a 2016
DHQ ta karrama Laftanal Kanal Abu Ali, yariman da Boko Haram suka kashe a 2016. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Ali ya jagoranci daya daga cikin gagarumin artabun da sojin Najeriya suka yi da Boko Haram a watan Fabrairun 2015, wanda hakan yasa suka kwace garin Baga a Borno.

A ranar 7 ga watan Nuwamban 2016, TheCable ta yi wata wallafa inda ta bukaci gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta sakawa wata barikin sojoji ko makaranta a Borno sunan jarumin da ya amsa kiran mahallicinsa a gaban daga.

Hakazalika, jaridar ta yi kira ga gwamnati da ta karrama Ali bayan mutuwar sa.

A ranar Asabar, hedkwatar tsaro cikin shagalin ta na cikar Najeriya 61 da samun 'yancin kai, ta karrama hafsoshin soji 12 da kananan sojoji 12 kan kwarewa da jarumtarsu.

Fatima Abu-Ali, diyar marigayin jarumin tare da taimakon matarsa, Samira Abu-Ali, su ne suka karba kambun girmamawan.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya maida wa Sanusi martani kan ikirarin cewa tattalin Najeriya ya kusa ya ruguje

A yayin jawabi a taron, shugaban ma'aikatan tsaro, Lucky Irabor, ya kwararo kalaman yabo da jinjina ga Laftanal Kanal din kan sadaukarwarsa, zakakurancinsa da kwarewarsa wurin shugabantar dakarun soji wuin yaki da ta'addanci a arewa maso gabas.

Irabor ya ce, wannan bikin lokaci ne da sojojin za su tuna da lokutan annashuwa da kuma wasu daga cikin dakarun da suka nuna kwarewa a filin daga.

Ya kara da jinjina wa matansu kan yadda suka sadaukar da rayukansu wurin hidimta wa kasa.

Shugaban ma'aikatan tsaron ya ce har kullum, dakarun sojin sun mayar da hankali wurin shawo kan kalubalen tsaron da kasar nan ke fuskanta.

2023: Ta yuwu Najeriya ta samu 'yan takara 2 marasa amfani idan aka dubi yanki, Sanusi

A wani labari na daban, Muhammadu Sanusi II, tsohon sarkin Kano, ya ce alanta mulkin shugaban kasa ga yanki zai iya sa kasar nan ta kare da 'yan takara biyu marasa amfani a 2023.

Kara karanta wannan

A shirye nake na taimakawa kasar Sudan don ta ci gaba, inji shugaba Buhari

A yayin jawabi a Arise TV a ranar Juma'a, Sanusi ya ce sau da yawa ya na kushe duk wata tattaunawa da za a yi kan yankin da ya dace ya samar da shugaban kasa, TheCable ta ruwaito.

Manyan jam'iyyu biyu na kasar nan na APC da PDP suna ta cece-kuce kan yankin da zai samar da shugaban kasa. Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya ya ce Najeriya ta na bukatar shugaban kasa wanda zai iya amfanar ta ba tare da duban yankinsa ba, TheCable ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel