Yadda sojoji suka bankado yunkurin ISWAP na kai wa tubabbun Boko Haram farmaki
- Zakakuran sojin Najeriya sun yi fata-fata da 'yan ta'addan ISWAP da suka kai wa tubabbun Boko Haram farmaki
- A fusace 'yan ta'addan suka tsinkayi inda aka bai wa tubabbun a Damboa tare da yunkurin kashe su tare da kama wasu
- Tuban manyan kwamandojin tare da wasu mambobin kungiyar bai yi musu dadi ba, hakan yasa suka kai musu farmaki
Damboa, Borno - Dakarun sojin Najeriya sun bankado wani hari da mayakan ta'addanci na ISWAP suka kai wa tubabbun 'yan Boko Haram a Damboa da ke jihar Borno.
TheCable ta ruwaito cewa, mayakan ISWAP din a ranar Lahadi sun hanzarta zuwa inda tubabbun 'yan ta'addan suke da masaukinsu.
Onyema Nwachukwu, mai magana da yawun rundunar sojin a wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce dakarun sojin rundunar operation Hadin Kai ne suka fatattaki 'yan ta'addan daga yankin.
Ya ce miyagun sun yi kokarin kai wa tubabbun 'yan ta'ddan farmaki ne domin su sare musu guiwa kan yadda suka mika wuya, TheCable ta wallafa.
"'Yan ta'addan ISWAP sun hango cewa babu nasara a al'amarinsu, lamarin da yasa suka kagauta wurin kai farmaki kan tubabbun 'yan Boko Haram da iyalansu," takardar tace.
"Wannan kuwa sabon salon tada zaune tsayen 'yan ta'addan na yin shi ne domin ganin sun rage wa tubabbun 'yan Boko Haram din karfin guiwa. Hakan kuwa ya na da alaka da yadda manyan kwamandoji da mambobinsu suka tuba.
“Bakin ciki tare da takaicin wannan lamarin ne yasa a ranar 2 ga watan Oktoba, 'yan ta'addan suka je da kudirin kisa ko kama 'yan ta'addan da suka tuba a Damboa. Zakakuran sojin Operation HADIN KAI wadanda suka bude wa 'yan ta'addan wuta, sun sa suka watse tare da barin kudirinsu.
“Rundunar sojin Najeriya na cigaba da tabbatar wa da jama'ar Damboa da kewaye kan cewa su cigaba da aiwatar da lamurransu na yau da kullum saboda dakarun za su cigaba da samar da tsaro ga dukiyoyi da rayuka.
"An bukaci mutanen gari da su samar da bayanai a kan lokaci kan al'amuran 'yan ta'addan da masu basu goyon baya."
2023: Ta yuwu Najeriya ta samu 'yan takara 2 marasa amfani idan aka dubi yanki, Sanusi
A wani labari na daban, Muhammadu Sanusi II, tsohon sarkin Kano, ya ce alanta mulkin shugaban kasa ga yanki zai iya sa kasar nan ta kare da 'yan takara biyu marasa amfani a 2023.
A yayin jawabi a Arise TV a ranar Juma'a, Sanusi ya ce sau da yawa ya na kushe duk wata tattaunawa da za a yi kan yankin da ya dace ya samar da shugaban kasa, TheCable ta ruwaito.
Manyan jam'iyyu biyu na kasar nan na APC da PDP suna ta cece-kuce kan yankin da zai samar da shugaban kasa. Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya ya ce Najeriya ta na bukatar shugaban kasa wanda zai iya amfanar ta ba tare da duban yankinsa ba, TheCable ta wallafa.
Asali: Legit.ng