Majalisar dattawa ta nemi Buhari ya fitar da N300bn don gyaran tituna a Neja

Majalisar dattawa ta nemi Buhari ya fitar da N300bn don gyaran tituna a Neja

  • Majalisar Dattawa ta bayyana bukata ga Buhari ta ware wasu makudan kudade don gyara tituna a Neja
  • Sun bayyana cewa, ana bukatar kudaden da suka kai N300bn don gyara da gina tituna a jihar Neja
  • Wannan na zuwa ne yayin da hanyoyi a jihar suka lalace kamar yadda sanata a jihar ya bayyana

Abuja - Majalisar dattijai a ranar Talata ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta samar da Naira biliyan 300 a matsayin kudin taimakon gaggawa don gyara munanan hanyoyi a jihar Neja.

Wannan kuduri na babban zauren ya biyo bayan wani kudiri kan lalacewar hanyoyi a fadin jihar Neja da toshe hanyoyin ta hanyar nuna rashin amincewa da direbobin tirela da direbobin tanka suke yi a cikin kwanaki hudu da suka gabata.

Yanzu-Yanzu: Majalisar dattawa ta nemi Buhari ya fitar da N300bn don gyaran tituna a Neja
Farfajiyar Majalisar Dattawan Najeriya | Hoto: dailytrust.com
Source: Facebook

Mataimakin Babban Bulaliyar Majalisar Dattawa, Sanata Aliyu Sabi Abudullahi, mai wakiltar Neja ta Arewa ne ya kawo kudirin, in ji rahoton The Nation.

Read also

PDP ta caccaki gwamna, mataimakiyarsa da kakakin majalisa bisa barin jama'arsu don tare wa a kasar waje

A cikin gudunmawarsa, Sanata Mohammed Sani Musa, ya zargi Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Raji Fashola, da nuna son kai a aikinsa na gina hanyoyi da gyaran hanyoyi a jihar Neja.

Idan na yi magana kan 'yan bindiga, kawuna za su gwaru, inji Sanatan Arewa

Dan majalisar dattijai mai wakiltar mazabar Kaduna ta Kudu, Danjuma La’ah, ya bayyana dalilan da ya sa ya zubar da hawaye a lokuta daban-daban a farfajiyar majalisa yayin da yake gabatar da kudiri kan hare-haren ‘yan bindiga a mazabarsa.

Dan majalisar na tarayya ya bayyana cewa wasu daga cikin abokan aikin sa na sanata suna tunanin ayyukan ta'addanci a Kudancin Kaduna batu ne na kudancin Kaduna kadai, SaharaReporters ta ruwaito.

Da yake magana, ya tuna lokacin da ya fada wa sanatoci cewa, akwai lokacin da dukkan mazabu 109 na sanata a kasar za su fuskanci matsala irin ta yankinsa, inda kuma ya ce yanzu hakan ya faru.

Read also

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun yi awon gaba da AVM Sikiru Smith (rtd) a jihar Legas

Rahoto: Halin da ake ciki na harin 'yan bindiga duk da katse hanyoyin sadarwa a Zamfara

A wani labarin, alamu sun bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da samun kashe-kashe da garkuwa da mutane a jihar Zamfara duk da katse hanyoyin sadarwa a jihar.

Yayin da katsewar da kokarin sojoji ya rage barnar 'yan bindiga tare da kashe su, wasu mazauna jihar sun shaida wa BBC Hausa cewa an ci gaba da kai hare-hare da sace-sacen a jihar.

Don haka, duk da rokon da suke yi wa gwamnatin jihar na tsagaita wuta, kamar yadda Gwamna Bello Matawalle ya bayyana a ranar 10 ga Satumba, 'yan bindigan sun ci gaba da kai hari kan mazauna jihar.

Source: Legit.ng

Online view pixel