Gwamnatin Kaduna ta ba da umarnin katse hanyoyin sadarwa a jihar

Gwamnatin Kaduna ta ba da umarnin katse hanyoyin sadarwa a jihar

  • Gwamnatin jihar Kaduna ta sanya sabbin dokoki a jihar don magance matsalolin tsaro da suka addabi jihar
  • An dakatar da ayyukan hanyoyin sadarwa da kuma dakatar da zirga-zirgan ababen hawa na daban-daban
  • Gwamnatin jihar ta jero sabbin matakan da ta dauka domin ganin ta samar da mafita ga matsalar tsaro

Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da dakatar da ayyukan hanyoyin sadarwa da takaita zirga-zirgar ababen hawa a yankuna daban-daban na jihar.

Wannan na zuwa jim kadan bayan da gwamnan jihar ya sanar da cewa, gwamnatin jihar ta nemi gwamnatin tarayya ta ba ta damar dakatar da hanyoyin sadarwa a jihar.

Gwamnatin jihar ta kuma ce an fara shirye-shiryen rufe ayyukan sadarwa a sassan jihar.

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida ne ya bayyana sabbin dokokin ga manema labarai a yau Laraba 29 ga watan Satumba.

Read also

DHQ ta karrama Laftanal Kanal Abu Ali, yariman da Boko Haram suka kashe a 2016

Da dumi-dumi: An katse sabis din layukan waya a jihar Kaduna
Taswirar jihar Kaduna | Hoto: dailynigerian.com
Source: Twitter

A cikin wata sanarwa da Legit.ng Hausa ta samo, kwamishinan ya ce matakan za su taimakawa hukumomin tsaro gudanar da ayyukan su a sassan jihar.

A cewar sanarwar:

“Za ku tuna cewa Gwamna Nasir El-Rufai ya sanar a cikin hirar da ya yi da manema labarai a jiya (28 ga Satumba 2021) cewa gwamnatin jihar ta nemi gwamnatin tarayya a hukumance da ta tilasta dakatar da hanyoyin sadarwa a sassan jihar da hukumomin tsaro suka gano cewa suna bukatar irin wannan matakan.
“Hukumomin tarayya da abin ya shafa a yau sun sanar da gwamnatin jihar Kaduna.
“A wani mataki na magance matsalar tsaro a halin yanzu a jihar Kaduna da makwabtan jihohi a shiyyar Arewa maso yamma da Arewa ta tsakiya, KDSG ta yi tarurruka da dama da hukumomin tsaro don daukar matakai masu mahimmanci don murkushe 'yan bindiga a maboyarsu.

Read also

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa na lalata, aure ya mutu a daren farko

“Sojoji da sauran jami’an tsaro suna kai hare-hare kan wuraren da aka gano. An shawarci gwamnatin jihar cewa wasu matakan yanzu sun zama dole saboda taimakawa kwazon wadannan hukumomin tsaro.
“Matakan masu zuwa za su fara aiki daga ranar Alhamis, 30 ga Satumba 2021: Cikakkun haramcin amfani da babura (Okada), na kasuwanci ko na kashin kai, na tsawon watanni uku a matakin farko. Hana mallaka ko amfani da muggan makamai.
“An yarda babura masu kafa uku su yi aiki daga karfe 6 na safe zuwa 7 na yamma. Dukkan babura masu kafa uku dole ne su cire labule. An takaita zirga-zirgar dukkan babura masu kafa uku daga magariba zuwa wayewar gari (7 na yamma zuwa 6 na safe).
“Duk ababen hawan da ake amfani da su don safarar kasuwanci dole ne a yi musu fenti mai launin rawaya da baki a cikin kwanaki 30. Ababen hawan da ke cikin ayyukan zirga-zirga dole ne su dauki ratsin rawaya da bakin fenti.”

Read also

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Hakazalika, gwamnatin jihar ta haramta jigilar dabbobi a ciki da wajen jihar, kana ta haramta sare bishiyoyi da ayyukan gandun daji a kananan hukumomin Birnin Gwari, Giwa, Chikun, Igabi, Kachia, Kagarko da Kajuru.

An kuma dakatar da kasuwannin mako-mako a cikin kananan hukumomin da ke gaba-gaba na Birnin Gwari, Giwa, Chikun, Igabi, Kajuru da Kawo na mako-mako na karamar hukumar Kaduna ta Arewa.

An kuma hana sayar da man fetur a jarkoki ko wasu mazubi a kananan hukumomin Birnin Gwari, Giwa, Chikun, Igabi, Kachia, Kagarko da Kajuru, da sauran batutuwan da suka shafi tsaro.

Ba mu ci ta zama ba: 'Yan sanda sun dukufa a aikin ceto wani babban soja da aka sace

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas a ranar Talata 28 ga watan Satumba ta ce bata ci ta zama, kuma ta tura dukkan zakakuran jami'anta don ganin an ceto AVM Sikiru Smith mai ritaya daga hannun 'yan bindigar da suka yi garkuwa da shi.

Read also

Gwamnatin Buhari ta amince maza su ke tafiya hutu idan matansu sun haihu

Mai magana da yawun rundunar sandan jihar, CSP Adekunle Ajisebutu, shine ya bayyana hakan yayin da yake mayar da martani kan sace babban hafsan na sojin sama, Daily Nigerian ta ruwaito.

Rahoto ya nakalto shi yana cewa: "Muna kan aiki don ceto shi."

Source: Legit

Online view pixel