Mutane 13 sun mutu a hatsarin mota a hanyarsu ta zuwa ɗaurin aure, ciki har da ƙanin ango da matarsa

Mutane 13 sun mutu a hatsarin mota a hanyarsu ta zuwa ɗaurin aure, ciki har da ƙanin ango da matarsa

  • Kimanin mutane 13 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon hatsarin mota a jihar Rivers
  • Rahotanni ya ce mutanen suna kan hanyarsu zuwa daurin aure ne a Imo
  • Shugaban karamar hukuma ya ziyarci wurin ya bada agaji wurin kai gawa asibiti

Rivers - A kalla mutane 13 ne suka riga mu gidan gaskiya a jiya sakamakon hatsarin mota da ya faru kusa da garin Akpoku-Udufor da ke karamar hukumar Etche a jihar Rivers, The Nation ta ruwaito.

Fasinjojin da ke cikin babban bas kirar Coaster sun baro garin Afara da ke Etche a jihar, suna kan hanyarsu na zuwa hallartar wani daurin aure da za a yi a jihar Imo da ke makwabtaka da su.

Mutane 13 sun mutu a hatsarin mota a hanyarsu ta zuwa ɗaurin aure, ciki har da ƙanin ango da matarsa
TaswirarJihar Rivers. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Amma kasa da mintuna 30 bayan motarsu ta hau hanya, ta yi karo da wani babban mota, hakan ya yi sanadin salwantar rayyuka a kalla 13 na matafiyan.

An kwatanta hatsarin a matsayin daya daga cikin mafi muni da suka faru a baya-bayan nan.

Kanin ango da matarsa na cikin wadanda suka rasu

Wani majiya daga yankin da abin ya faru ya ce bus din da babban motan sunyi karo ne gaba-da-gaba kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ya ce kanin ango da matarsa na cikin wadanda suka rasa rayukansu.

Mutane 11 sun mutu nan take yayin da sauran suka cika a hanyar kai su asibiti.

Wata majiya daga karamar hukuma ta ce shugaban karamar hukumar Obinna Anywanwu ya ziyarci inda abin ya faru ya kuma taimaka wurin kai gawarwakin asibiti.

Kakakin yan sandan jihar Rivers, Nnamdi Omoni ya tabbatar da afkuwar lamarin amma ya ce gawarwaki biyar aka gano a wurin da hatsarin ya faru.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan bindiga sun kai farmaki coci, sun sheke mai bauta

An kuma, wani mutum ya jefi Shugaban Faransa, Emmanuel Macron da ɗanyen ƙwai

A wani labari daban, shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya ji saukar kwai a kafadarsa bayan ya kai ziyara wani gidan cin abinci a kasar ta Faransa.

Kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito, bayan jifar sa da kwai da wani ya yi, ya sauka a kafadar sa sannan ya fadi kasa ba tare da ya fashe a jikin sa ba.

Ya kai ziyara wani wurin cin abinci da Otal ne dake kudu maso gabashin birnin Lyon a ranar Litinin kamar yadda AFP ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel