Kaduna: Miyagu sun sheke mutum 8 a farmakin martani da suka kai Zangon Kataf

Kaduna: Miyagu sun sheke mutum 8 a farmakin martani da suka kai Zangon Kataf

  • A wani farmakin mayar da martani, wasu miyagu sun halaka rayuka takwas a yankin Kacecere da ke Zangon Kataf
  • Hakan ya biyo bayan wani farmaki da 'yan bindiga suka kai Madamai inda suka halaka rayuka 34
  • Gwamnan Kaduna ya yi Allah wadai da farmakin da ya bar gawawwaki takwas da wasu mutum shida a jigace

Kaduna - A wani harin mayar da martani, wasu mutane da ba a san ko su waye ba a kauyen Kacecere da ke karamar hukumar Zangon Kataf ta jihar Kaduna sun halaka rayuka takwas, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, a wata takarda da ya fitar, ya ce wannan harin mayar da martani ne wanda aka fara a kauyen Jankasa da ke karamar hukumar Zangon Kataf inda aka kashe wani Yakubu Danjuma tare da halaka wasu mutum 34 da ke Madamai a karamar hukumar Kaura ta jihar.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Kaduna: Miyagu sun sheke mutum 8 a farmakin martani da suka kai Zangon Kataf
Kaduna: Miyagu sun sheke mutum 8 a farmakin martani da suka kai Zangon Kataf. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC
"Farmakin da aka kai wuraren nan biyu, jami'an tsaro sun gano cewa shi ya janyo farmakin mayar da martani da wasu suka kai yankin Kacecere wanda ya bar rayuka takwas a mace, mutum shida da raunika da kuma gidaje da aka kone," Aruwan yace.

Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana damuwarsa da alhini kan rahotannin kuma ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan mamatan.

Gwamnan ya yi kira ga hukumomin da suka dace da su tabbatar da an dauka dokar gaggawa tare da yin kira ga yankunan da su guji kai harin martani .

Ya kara da kira ga hukumomin tsaro da su tabbatar da sun binciki lamarin, Daily Nigerian ta wallafa.

A yayin rubuta wannan rahoton, dakarun soji da jami'an 'yan sanda suna aiki a wurare daban-daban kuma za su sanar da jama'a cigaban da aka samu.

Kara karanta wannan

Hotunan budurwar da ta rasu ana sauran mako 5 aurenta sun gigita jama'a

Sojojin Nijar sun ceci sojin Najeriya da 'yan bindiga suka kai wa farmaki sansaninsu a Sokoto

A wani labari na daban, dakarun sojin kasar Nijar sun ceci sojojin Najeriya 9 wadanda suka tsere yayin da 'yan bindigan daji suka far musu a Sokoto.

Majiyoyi sun sanar da Daily Trust cewa an ceci sojin Najeriyan a Basira, wani kauye da ke kan iyaka karkashin yankin Hodan Roumdji a jamhuriyar Nijar a ranar Juma'a.

Daily Trust ta ruwaito yadda 'yan bindiga suka kai farmaki sansanin hadin guiwa na sojoji da ke sansanin Burkusuma a karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto inda suka kashe jami'an tsaro.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel