Manjo a soja ya maka rundunarsu da bankin FCMB a kotu kan daskarar da asusunsa

Manjo a soja ya maka rundunarsu da bankin FCMB a kotu kan daskarar da asusunsa

  • Wani soja ya shigar da rundunar sojin Najeriya a kotu bisa daskarar da asusun bankinsa
  • Ya nemi kotu ta ba rundunar soji da wani banki umarnin dawo masa da kudadensa
  • Ya kuma nemi kotu ta hana bankin da rundunar soji taba kudadensa da daskarar da asusunsa

Abuja - Wani Manjo a rundunar soji, Akeem Adeeogba Osenifor ya maka sojin Najeriya da bankin FCMB kan wasu kudade.

Manjon ya zargi rundunar soji da bankin da daskarar da asusun bankinsa tare da binciken gidansa ba tare da umurnin kotu ba, SaharaReporters ta ruwaito.

A cikin karar da ya shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, jami’in ya roki kotun da ta umarci wadanda ake kara su biya shi wasu makudan kudade da suka kai N16.6m a matsayin kudin da yake zargi an sace daga gidansa tare da wasu kadarori masu daraja.

Read also

Yadda jami'an tsaron UNIMAID suka afka dakunan kwanan dalibai mata, suka damke masu zanga-zanga

Manjo a soja ya maka rundunarsu da bankin FCMB a kotu kan daskarar da asusunsa
Sojin Najeriya | Hoto: thisdaylive.com
Source: UGC

Lauyan sa, Mike Ozekhome, SAN ya gabatar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1104/2021 da ke neman a bi masa kadunsa kan take hakkinsa da aka yi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai shigar da karar ya kuma ce yana son kotu ta umarci Sojin Najeriya da su cire 'Post No Debit' (PND) da aka sanya a asusun sa da kuma umartar tilas ga FCMB ta nemi afuwar sa a cikin akalla jaridu uku na kasa saboda cin zarafin da aka yi masa ba tare da bin tsarin doka ba.

Ya nemi a ba da umarnin hana wadanda ake kara, wakilan su, ma’aikatan su, masu binciken su, da sauran masu ruwa da tsaki kan cire shi a PND ba tare da ingantaccen umarnin kotu ba.

Kwamandan NDA ya yi wa majalisa bayanin halin da ake ciki kan harin 'yan bindiga a NDA

Read also

'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro 17 yayin harin Sokoto, Ɗan Majalisa

Kwamandan makarantar tsaro ta sojoji wato NDA, Ibrahim Yusuf, ya yi wa Kwamitin Tsaro na Majalisar Wakilai bayani game da harin da wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka kai makarantar.

A yayin harin a ranar 24 ga watan Agusta, an kashe jami’an soji guda biyu sannan an yi garkuwa da daya, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya ba da rahoton cewa kwamandan ya gana da kwamitin ne cikin sirri, kamar yadda kwamandan ya ce an tsara takardun da za a gabatar wa membobin kwamitin.

Mista Yusuf kafin taron ya shiga ganawar sirri, ya ce zai yiwa kwamitin bayani kan kokarin da sojoji ke yi na kubutar da jami'in da aka sace.

Ya bayyana cewa Babban Hafsan Tsaro, Lucky Irabor, ya ziyarci inda aka kai harin a ranar da abin ya faru, ya kara da cewa wasu manyan sojoji da ke aiki da wadanda suka yi ritaya su ma sun ziyarci wajen.

Read also

Gwamnatin Amurka ta tattara shaidu 6,700 don tabbatar da laifin Abba Kyari

Don haka Shugaban Kwamitin, Babajimi Benson (APC-Lagos), ya nemi 'yan jarida da ke wurin da su fice, amma ya ce kwamitin zai bincika kan kokarin da ake yi na ceto jami'in da aka sace.

Majalisar dokoki ta tsaurara matakan tsaro kan wata zanga-zangar ma'aikata

A wani labarin, wani rahoto da jaridar The Nation ta fitar na nuni da cewa an tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen Majalisar Dokoki ta kasa domin dakile wata zanga-zangar da wasu masu taimaka wa majalisar suka shirya.

Majalisar a safiyar ranar Litinin, Litinin, 27 ga watan Satumba, ta tsaurara matakan tsaro bayan ma’aikata karkashin kulawar ma’aikatan majalissar suka tunzura don gudanar da zanga-zanga kan batun albashinsu.

Jami'an tsaro da suka hada da masu kwantar da tarzoma da 'yan sanda na yau da kullum, ma'aikatan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da sauran jami'an tsaron majalisa duk hallara don kula da hanyoyin shiga da fita daban-daban a harabar majalisar.

Read also

'Yan sanda sun kama tsohon ɗan majalisa da mutane 2 bisa zargin harkar ƙungiyar asiri

Source: Legit Newspaper

Online view pixel